Lyrics
Kyautar so nabaki, domin ki wuce aro
Ni mai zaki bani, Allah yasa nayi farin jini
Kyautar so na baka, komai duka na tattaro
Allah yasa zaka dauka, yaro mai farin jini
Sai murna nake a yau nacika buri
Nayi gamo da sahiba mai kyan tsari
Ta shiga zuciyata, tasa annuri
A fagen so ku dubi na zarce gori
Karaya akewa dori
Marar ji saida mari
Ya Allah tsareman dukkan sharri
Soyayya mu zama cikin masu sukuni
Naga farincikin dake sa ayi kwalla
Dan a isar da sako kesa ayi shela
Dan ayi tarbiyya ake rike bulala
Jirgin so nahau a yau sama na lula
Alkawarin so na kulla
Soyayya na kulla
Yau sai godiya nake a gurin Allah
Dan wannan farincikin shi yabani
Kyautar so nabaki, domin ki wuce aro
Ni mai zaki bani, Allah yasa nayi farin jini
Kyautar so na baka, komai duka na tattaro
Allah yasa zaka dauka, yaro mai farin jini
Kafin wani yace maki "Ina-ina masoyinki?"
Kafin ya rufe baki za'a ganni na fito
Dan ke kadai nasa raina bana yin bulayi
Safiya, dare zuwa rana ke na ambato
A cikin raina kin aje hoto
Da soyayyarki banayin koto
Ko an daure sonki can sama na reto
Ni zan takalo in hau koba tsani
Soyayya ruwan zuma ce, nashata gani kwance
Masoyi ya asirce ni, bani yin gani
Wallahi nayi dace, nazama abin kwatance
Sam bani bada rancen masoyi ba kun gani
Ni dakai muka dace
Da farar zuciyace
Masu bakin hali, hanya tasu mun kauce
Allah ne ya yarda mun kece raini
Kyautar so nabaki, domin ki wuce aro
Ni mai zaki bani, Allah yasa nayi farin jini
Kyautar so na baka, komai duka na tattaro
Allah yasa zaka dauka, yaro mai farin jini
Allah yasa nayi farin jini
Written by: Umar M Shareef