Music Video

Music Video

Credits

Lyrics

Na fada na kara
Nima na riga na furta
Na riga na tsara
Na riga na shirya
Na fada na kara
Daga ke ba kari
Na fada na kara (na kara)
Daga kai ba canji (ba canji)
Yadda dai kinka kin na gode
Sirrikanki gare ni kin bude
Nagani duka na rude
Nima nawa gareki zan fede
Yarda takai yarda
Ni da ke babu boyen sirri
Abun nema ya samu
Zuciya ba abunda yake damu
Yiriyiri kawai ya rage mu
Dauren aure Allahu ya kai mu
Daga zarar kowa ya shaida
Soyayya ba sauran buri
In kai baiwa Allahu zabi shikenan
Ka huta ba ka ba wahala kenan
Kai ta adu'a sai kadan yi jira sanan
Hakuri matakin na cin nasara kenan
Tabbas komai lokaci ne
Allah sa muga alkairi
Yaushe ne? Yaushe ne auren mu masoyina?
Yaushe ne za'a sa ranar mu masoyina?
Yaushe zamuje ga gano dangi da iyaye na?
Yaushe zaka kawo kudi gidan mu sadaki na?
Wallahi ni dai na kosa
A cikin kawaye in wuce gori
Bazan yi aure idan ba dake ba
Bazana goyi 'dan da ba naka ne ba
Duk wace ta kirani ma bazana zo ba
Komai ake nuna min bazan gani ba
Kauna ta kai kauna
Kai ne karshe kaine fari
Written by: Shareef studio, Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...