Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Umar M Shareef
Umar M Shareef
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Umar M Shareef
Umar M Shareef
Composer

Lyrics

(Rub Master)
Idan na rasa ki baza na ji dadi ba
Idan na rasa ka baza nayi aure ba
In na rasa ki baza na ji dadi ba
Soyayya jigon rayuwa ta
Nima in na rasa ka baza nayi aure ba
Soyayya jigon rayuwa ta
Zo na baki guri zauna
Babu kamar ki a kalbi na
Ke zan nuna wa dangi na
In fada masu nayi mata
Tuntuni na gama tari na
Na zo gurin ki mu tattauna
Batun auren mu muradina
Tunda dai mun daidaita
In na rasa ki baza nayi aure ba
Don kece warakar damuwa ta
Ni, na yarda na zam mai daki
A gidan inyi maka aiki
Aure indai da sadaki an gama komai
Kai zaka zamo mai mulki
In hada maka rigar saki
Ka saka ta ka hau kan doki
Ka zama jarmai
Indai da akwai ka basa mini komai ba
Don kaine ka zamo garkuwa ta
In na rasa ki baza na ji dadi ba
In na rasa ka baza nayi aure ba
Soyayya jigon rayuwa ta
Soyayya jigon rayuwa
Na hango ki a sahun gaba
Cikin matan kece gaba
Dukan sauran basu kai ki ba
Sun biki a baya
Su duka da yan uba
Ke suka martaba
Kin zama jagaba
Suka ce basu hangi kamar ki ba
Ko manyan basu fiki da komai ba
Shiyasa na kira ki da yar autar mata
Zan hau in ka yarda
Doki na kara danda
Da gudu in shigo fada
In fadi cikin wasa
Siyan nagari kudi a gida
Mai kyau baya yimin tsada
Ayiri-yiri ranar murna
Kyautar kaina na bada
Bazan so a saka shi da nisa ba
Ranar auren mu da kai ya kinmata
In na rasa ki ina zan kwana, masoyiya?
In na rasa ka a daina batu na, an rufe babi na
Wanda yaso jin labari na, yazo gun ki ya zauna
Babu abinda ya boyu a kaina, kasan duka sirri na
Tun haduwar mu ba kiyi mini karya ba
Ai tun haduwar mu ba kayi mini karya ba masoyi na
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...