Music Video

Music Video

Lyrics

Bani ganin nisan tafiya kaunace tasaka
Inda naje ke zana ishe kiyimin bangajiya
Bani ganin nisan tafiya kaunace tasaka
Inda naje kai zana ishe kayimin bangajiya
Uhh, uhh
Na fito fili na tsaya, sonki shi nasaka a gaba
Amshi sona kiyi ajiya, tunda banason taruba
Bani naki nima in rike haka zai zo maruba
Alkawarin juna mu rike muyi so gangariya
Uhhh
So haduwata da kai ban son rabuwa da kai
Muyi aure ni dakai farin ciki na sai da kai
Duk inda zanje sai da kai, kana a zuciya kai da kai
Inda nataka tare muke a zuciya nayi ajiya
Ehh
Sonki shine yasa naji ni zan iya komai
Na tattaro na kawo gabanki dukan mukamai
Sirrina hannunki yake duka muhimmai
Yarda dani ni nayi miki juna muyi rakiya
Soyayya gata a fili a ido bata buyaba
Itce daban ne da kwali nauyinsu bai zama dayaba
Dakinda babu makulli ajiya ciki bazan yiba
In da nadau matsayin ka nasa kafafu basu zuwa
Bani ganin nisan tafiya kaunace tasaka
Inda naje ke zana ishe kiyimin bangajiya
Written by: Umar M Sharif
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...