Music Video

Featured In

Credits

PERFORMING ARTISTS
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Songwriter

Lyrics

Ku gyara zama zana fada muku yau wasa an fara Shanye rubutu hidima da kudi sai in an tara Nayi rawata tai kyan kalla amma kan rera Mai iya zance komai zai furta sai ya gyara Shi gizo karya a kasan shi dayi magi ya kara Gamu biki wanda ado mai kyau wane yar mora Dan hidiman yau dole ka nema kudi Inda zuma na gamsa dauka madi San ya ido inda wata gefe zaka zaka gano zara Dole ruwa za ya fito a jikin baure an sara Shi rufa laya na badukku ne duba shi wajan kira Za kaga kwaya a ciki na gyada inde ka bara Neman sauki niyan tuba miyo kaffara Nawa rabon ya rantse a ruwa na sama allura Inda kazanta gu sai kaga 'kuda Banda wurin yawo na zaba gida Komai girman zakara a kace toro ya fishi Banda abin dai kunne ya jiya wane yan amshi In ka jiyo kukan gauraka taro ya tashi Sai naji shago shi ne yaka shanye zafin naushi Ko makaranta can baya ke 'kyele mai fashi Jaddada kaifi na wukake ne tsini sai mashi Madugu shi 'daya ke jure tafiya Ga wani na ladabi dan gyara miya Naga da ance aka yin shakar kamshi ko iska Za aga haske fitila a duhu inde an haska Mai magagi inde yaji feshi sai ya farka Jaddada kalmar ga hawa sama tsani sai antaka Cewa manoma su fito da Iri anyi ruwan shuka Sanda ake so arufe daki ba'a bidar 'durka Duk yanayi daya ne kwarya da duma Gun kwari akushi ya dara su kuma Kai mai wasa da biri shi ke burkata bakaka Ga mafarauta da maciji nan kowa na shakka Soja da kwazo ni sai na hange shi saman tanka Gaida mazaje a wurin mata ne akasan dilka Allah tsara tso-tsai a cikin waka in yaba hankaka Karkayi burga da abin wani sai in ya zam naka Cikar matsayin nono a hada da fura In naci kifi bana shan madara Illar aljan ka taba shi ka tun kari ma kwan cinka To haka dodo ka taba shi a daji sai ya karka Kayi gudu kakka du kani ka kakkare kukan ka Ba wani motsi dan ba aikin yan sara suka Ga mafita dai adu'a zakai baya jin duka Gwanda ka roka duk inda kake shi sai ya jika Ba nasara a gudu in ba mafita Dukka na 'daure yana San yai sakata Yara ku kamasu ku kaisu gida kura ta kwance Dan mazari ya rike kan mota amma ta kwacce Nuna iyawa da yake sanyi ya da san zarce Sanya kulawa acikin tafiya rauni ka kauce Duk mai zari baya hadama wannan ya dace Nema kadan karka zu bawa baki sai ya huce Kaji fushi baya kyawo ga damo Nai magana kunne ya amsa awo Nura da kyau karka sakar wa doki dukka limzami Masu idanu sune suka gane girman rami Masu gwalando su za su fada ma zafin fami Tambaya yara dadin goyo raino sai momi Duk maraji shine be san bari ba Zanta zubo baiti ba zan gaji ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out