album cover
Kece
20,219
Pop
Kece was released on April 5, 2018 by Premier Records as a part of the album Iconic Sounds of Africa, Vol. 67
album cover
Release DateApril 5, 2018
LabelPremier Records
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM100

Credits

PERFORMING ARTISTS
Hamisu Breaker
Hamisu Breaker
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Hamisu Breaker
Hamisu Breaker
Composer

Lyrics

Eh! a duniya ke kika zama farin cikina
Idan ba ke wa zana bai wa ƙauna
Farin cikina kin zama jinin jikina
Idan da so ƙauna ba ta kai ni rana
Kin zamma jigo hasken idaniya ta
In na rasa ki wa zata ba ni gata
Ni ke nake wa kallon sarauniyata
A gurbin zuciya ba ni ajje wata
Ki dawo in da nake don mu zanta
Mai sona mai kyan hali nagarta
Baiwar Allah ke ce cikar muradi
Wanda ke sonki na so shi don zumuɗi
Ki minni uzuri kar kice nayi kauɗi
A kanki ko me na yi so ya ingizani
Idan na zauna ni ke nake tunani
Ko cikin bazara damina da rani
Wayyo Allah da ma za ki tunani
Kamar yadda nake miki sai ki so ni
Idan na kalle ki kina rikirkita ni
A zuciyata ina sonki ba ma'auni
Ba ni dama ya masoyiyata
Mai rabon ya ga badi zai gani gwanata
Cikin masoyanki a yanzu na yi rata
Tunda ni zan iya ba ki rayuwata
Taho garen zana riƙeki ba mugunta
Ni fa nace ke ce masoyiyata
Abin da soyayya ta sanar aminta
Tausayi ko ko zamanmu kai da fata
A gidan duniya samun masoyi daɗi
Rashin masoyi shi ke cire nishaɗi
Da kin kirani nan take zani amsa
Aurenki nai niyya kar kice na fasa
Za ki zam mata tawa rai ya ƙunsa
Duk kamanni naki sunyi ba makusa
Walwalata abar alfaharina
Sonki yai mini dauri irin na gwarmai
Ni fa sonki biyayya kawai nake mai
Sonki yai mini daɗi inai da mai mai
Ni ban da burin da ya kai in baki komai
Wanda ke ƙin ki a yanzu zani far mai
Na faɗa soyayya ruwan zuma ce
Wassu na kallo na kamar a zauce
Darrajar soyayya ko ba kwatance
Wanda ke so shi ya sanshi ko a zance
Masoyiyata karɓi uzzurina
Kar ki bar sonki ya zamma ajalina
Farin cikin soyayya ta zamma ƙauna
Wallah kan sonki kawai na manta kaina
A ko da yaushe hotonki na hanuna
Duka abin da kake so yana gareka
Ina sonki fiye da so hakan na saƙa
Abin da ranka yake so idan ya so ka
Yana da daɗi ni haka nan na ɗauka
Shi yasa soyayarki tai ta girma
A zuciya ta komai ta fi shi ƙima
Written by: Hamisu Breaker
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...