Lyrics

Beat amjad records Kalmar tana nufin abinda zuciya ta so Amma a nawa bangaran rai ne da rayuwa Sone lagwan mutane biyu inda shakuwa Mai kama dan adam da aljan da beguwa Domin mu gane so sai mun kara nutsuwa Dan dole dole so shi ke kaimu kokuwa Ena da tambaya menene farin ciki Mene bakin ciki ni so zana sa ciki Shi so baya duba girma Duk tsanani ya saka fama Ba talakan garin mu ba basarake bare hukuma Kai shi so daban yake Ba labe ko ko a fake So bai san gari ba zai kaika ena zama yake Kalamansa da yawa Kullum suyi ta karuwa Sun kai koli koli har sun samin kishirwa Eh kai so dakai nake Ena kake ena tambaya gunka da munyi haduwa Nagano masoyi kullum shi in ya tashi bacci Burinsa dai masoyiya karta kara kunci Sai ya lalubo waya ya kira shin kinci abinci Ba damu kansa ya ciba sai in gwanarsa taci So sam baida tausayi En yayi tabargaza amsar sai ta bada nayi Ba tsoro yake ba shima Sannan bai gudun husuma Zai iya tada yan adam Duk tsaye dan yana da girma Kullum in ena tunani Sai in bawa so maauni Amsa ta gareshi kullum sai ta fito da rani Ni ban gane so ba Ban san ya yake ba Abinda na dan fahimta kansa ne ban rufe ba Kalmar so tana girma Tanada da fadi Cikin ta akwai nishadi akwai nau i na fadama Nima dalibi nake Sannan bincike nake Kullum nema nake en hujjojin da zan ruke Ba dare da rana Na tambayawa kaina Shin menene so menene mahadi na Amsa guda nasan da so sila ne Kuma mahadi ne ga wanda duk ya gane In da lafiya a duniya Ko ba lafiya a duniya Duk girman zamani ko kuma karni Nasan bazaa rayu acikinsa babu so Se dakai Midgetmix
Writer(s): Hamisu Yusuf Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out