Lyrics

Abinda yake raina zana fitar in huce takaici Soyayya ke damu na zana fada bazan boye ba Nima abinda yake raina zana fitar in huce takaici Soyayyar ki a raina zana aje ba zata fice ba Hmmm, alamar tambaya tana ga mai yawaita tunani Musamman in ya shiga halin soyayyar zamani Yau gani cikin ta na rasa wanda zai fidda ni Sai kai masoyina wanda muka yi kyau da kamanni So a aikace, fayyace, yafi dace Ni a mutumce, kai zance ban canzawa Na gamsu da surarki, tsarinki har kyawunki Nima ina sonki, kwatankwacin kalaman baki Kallon so ya tsuma ni har nayi ra'ayin kaunar ki Ni dake in muna tare, babu mai raina ki Na rike kauna tarayya ta zauna Nayi shiri na zan kare dukka hakkin ki Rawa da girgiza zanyi gabanka in jujjuya Zanyi maka albishir kayi dace da mai tarbiyya Sannan zan zame maka farin ciki na nan gidan duniya Nafi kowa saninka cikin abinci kafi son taliya Zanyi rubutu, karanta ka fahimtu Na ilmintu a sonka nayi morewa Ko a kwatance banda yake nayi godiya Na kara hasashe, babu yake gun kwalliya Zabi na kece da gani babu tambaya Dawisu gurin ado babu yake kyan duniya Taho mu zauna In baki kauna Taho ki rike Masoyiya
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out