Credits

PERFORMING ARTISTS
Umar M Sharif
Umar M Sharif
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Umar M Sharif
Umar M Sharif
Composer

Lyrics

[Verse 1]
Kallon so nake maka, aha
Kallon so nake miki idanuwana
Su ke gwada mini da kyau kike
Kallon so nake mika idanuwana
Su ke fada mini da kyau kake
[Verse 2]
Da na fito 'yan mata ni dai suke jira
Kowacce ta tunkaro ni da kokon bara
Sun ce da ni so, na ce musu su yi hattara
Don na riga na yi nisa ba ni jin kira
Na ba da kaina a gare ki zo sarauniya
[Verse 3]
Kogi na soyayya can cikinsa ni nai nutso
Domin na burge ka masoyi nake yin kitso
Dube ni sosai kara masoyi na matso
In na aure ka 'ya'yana sun yi dacen tsatso
Na san za su yi alfaharin zuwansu duniya
[Verse 4]
Gajimare ya yi lif-lif da kyan gani yake
A sama tsuntsaye zagaye kawai suke
Suna ta hira a kan so kamar da mu suke
Na sanya kunne sosai zancen hakan yake
Kifin da ke ruwa ya san da mu a soyayya
[Verse 5]
Kallon so nake maka idanuwana
Su ke fada mini da kyau kake
[Verse 6]
Eh! Kallon so nake miki idanuwana
Su ke gwada mini da kyau kike
[Verse 7]
Ka zama abin kallo na mai sa ni farin ciki
Sam ba ka sa mini haushi bare bakin ciki
In an kira ni iri za a ce da kai taki
Da kai kadai zan zauna shiru cikin daki
Komai ka sa ni na yi maka babu jayayya
[Verse 8]
Allah ya ba ni ke na zamo cikin sa a
Ni ma sa ar na yo dole zan yi ma da a
Ko yaushe kun ga zam zama cikin yawan fara'a
In har ka ce da ni e, gare ni ba a'a
[Verse 9]
Babu ya ni rawar gani, na rike addu'a
Wanda yai haka sam ba shi babu jin kunya
[Verse 10]
Kallon so nake miki idanuwana
Su ke gwada mini da kyau kike
[Verse 11]
Kallon so nake maka idanuwana
Su ke fada mini da kyau kake
[Verse 12]
Da kyau kike (Da kyau kake)
Written by: Umar M Sharif
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...