Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Composer

Lyrics

[Verse 1]
Eh! lokacinki ne ya yi amarya 'yar amana
To ki je ki zauna da miji aure ibada ne
[Verse 2]
Iye! Mai zuban basira Allah da kai na fara
Na taho da koko bara nake tabara
Wakar da za na rera sai ka nufa na tsara
[Verse 3]
Zan yi ta ba gadara farin ciki amarya
Wasu sun iso ga wadansu na a hanya
Za na bude murya kira ki daura niyya
[Verse 4]
Tarkonki ya yi kamu, ko ba a so a ji mu
Tilas gari a bar mu don ga mu ga masoya
[Verse 5]
Babu ke a yau babu gantali a titi
Kin ga ke da angonki ni nake wa baiti
Ina da sahibata na kasa boye sonta
Me za na je na furta ban shawara amarya
[Verse 6]
Tunda duk abin cewa yanzu na gare ki
Me kika ji me kika yo gani a daki
Ango ya zo da harka yi mai miya ta kuka
Domin rana ta wanka ai cibi ba ya buya
[Verse 7]
Babu kyau yawan yin kace nace akalla
Yinsa a zaman tare ke haifar da illa
Yau ga wadansu dangi sun bar zuma a kungi
Haka suke da dagi yaransu na hamayya
[Verse 8]
Bar fushi yawan yinsa bai kama da ke ba
Bai kamata ki dau zuga ta 'yan uba ba
Don ba su so ki zauna shi ne na zo mu gana
Ki dauki duk batuna mai kinku zai ji kunya
[Verse 9]
In batu na sone kowa akwai gwaninsa
Wassu sun bi waina wadansu sai gurasa
Ke dai kin kama naki, ya zama mallakinki
Aiki yana gareki an so ki mai biyayya
[Verse 10]
Wasu cusa kai suke yi don a so su
Mai kamar zuwa kan aikawa da ki bar su
Ke ga wuka da nama rike ki ja ki kama
In kika yo zalama to zai fi kyau da suya
[Verse 11]
Je gaban gwaninki kawai ki yada zango
Inda dankali gobe za ki yo da rogo
A gaskiyar bayani fuskarki babu muni
Kin zarce a yi raini kin haskake alkarya
[Verse 12]
Yau da kin fito za na ce saura su koma
Kar ki fara aiki da za ki yo nadama
Wannan rana gareki ta sa ni tausayinki
Je kar ki taka birki dauko tufa ki sanya
[Verse 13]
Inda za ki je can shi ne gidan zamanki
To ki duba shuka in an zubanta taki
Zancen ga za ki auna sai ku yi zaman lumana
In kin ga wata rana yaranki za ki goya
[Verse 14]
Dan abin da yaz zo da shi taba ki lasa
Tunda ya zame ke kin zama shi ku nisa
In dai gyaran gida ne aikin da za ki yo ne
Angonki mai fita ne gurinsa tausa murya
[Verse 15]
Hudubar iyaye akanki dinga bita
Duk da mai sani ce ke baya kin karanta
Zan so ki kara himma nutsa cikin hirama
Sai ki gam asalama in kia kyauta niyya
[Verse 16]
Na taho ina gangara na rufe waka
Za na bar wasika in kuka bani fuska
Alfarma ku yi gare ni, in kun ji kun tuno ni
Ku yi addu'a gare ni kwalla ta bar kwaranya
Zunnuban da ke kai na rabbana ya yafe
Nan nake tsayawa na bar ku sai da safe
Written by: Isa Gombe, Nura M. Inuwa, Rr
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...