album cover

Fatima

4,971Easy Listening2020
album cover
Fatima was released on February 1, 2020 by Jita Recoed as a part of the album Jita
AlbumJita
ReleasedFebruary 1, 2020
LabelJita Recoed
BPM
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy

Lyrics

[Verse 1]
Yaraye Iye, ayye yaraye iyeh
Sannu sarauniya Fatima ke ce adon gari shalele
Yaraye Iye, ayye yaraye iyeh
Sannu sarauniya Fatima ke ce adon gari 'yar lele
[Verse 2]
Fatima murmushi, Fati da shi aka sanki ne (Nana Fatima)
Ta Iya kwalliya, labarin aka ba ni ne (Nana Fatima)
Ido ya gani na tabbata ai haka ne
Kin zama daban mata suna son su ganki ne
[Verse 3]
Kin zam sarauniya sunan ya zama naki ne (Nana Fatima)
Tauraruwar gari idaniya na ganinki ne (Nana Fatima)
Kin zama jauhari Fatima Allah ya ba ki ne
Dagwas-dagwas take, Fatima ya za na ganki ne
[Verse 4]
Gida da Fatima na yarda wannan gidanmu (Nana Fatima)
Gidan da babu ke Fatima wannan gidansu ne (Nana Fatima)
Kina da kwar jini Fatima launin idonki ne
Na mi ki tambura Fatima domin isarki ne
[Verse 5]
Mu yi mata gaisuwa ta girmama Nana dole ne (Nana Fatima)
Lakaninki autar mataye za su bi ki ne (Nana Fatima)
Su suna a baya kina a gaba matsayinki ne
Kin cika kin isa, Fatima ai girmanki ne
[Verse 6]
Kainuwa dashen Allah Sarki zamaninki ne (Nana Fatima)
Ga farar diya da farin hali Nana Fatima (Nana Fatima)
Ga mu mun taho don gaishe ki Nana Fatima
Zakara yana neman sa a Nana Fatima
[Verse 7]
Damina tana neman rahama Nana Fatima (Nana Fatima)
Sarakuna suna neman darajar Nana Fatima (Nana Fatima)
Yara ma suna neman addu'ar Nana Fatima
Mata suna da burin su yi kyawun Nana Fatima
[Verse 8]
Maza suna bukatar a gidansu su ga Fatima (Nana Fatima)
Duniya tana yin alfahari da Nana Fatima (Nana Fatima)
An tabbatar kura ba ta cin Nana Fatima
Zakuna suna kuma gaishe ki Nana Fatima
[Verse 9]
Farin jininki ya wuce labari Nana Fatima (Nana Fatima)
Ga azarbabin jitata ce Nana Fatima (Nana Fatima)
Tafiyarki daban Fatima ai halinki daban
Zamanki daban Fatima tashinki daban
[Verse 10]
Magana daban Fatima sakonki ya daban(Nana Fatima)
Tsarinki yai daban da na su komai daban-daban (Nana Fatima)
Jikinki na daban ga ilimin Fatima daban
Mai daban-daban Fatima kin sha daban-daban
[Verse 11]
Kalarki daban Allahu ke ce ya ba daban (Nana Fatima)
A gaida Fatima 'yar asali ce Fatima (Nana Fatima)
Kyawu yana zuba Allahu Ya ba ki Fatima
Farin idanuwa Allahu ke ce Ya karrama
[Verse 12]
Akwai farin hakori yana da kyalli na Fatima (Nana Fatima)
Kayan ado akwai kala-kala gunta Fatima (Nana Fatima)
Leshi yai mata kyau bare atamfarta Fatima
Tana shigar abaya ta sanya shaddarta Fatima
[Verse 13]
Ga zobuna a hannu sun mata kyawu Fatima (Nana Fatima)
Saka zinariya ki sanya gwal kin ji Fatima (Nana Fatima)
Kin yi kyau a doki ki tuka mota Fatima
Shiga ta birni tai miki kyawu Fatima
[Verse 14]
Ba kama ta jahilci daga an ganki malama (Nana Fatima)
Ga zubin sarauta kin dace don ko kin kama (Nana Fatima)
Makiyanki ma Fatima dole su sallama
[Verse 15]
Kin yi iliminki
Rabbana Ya ba ki
Ba a tseguminki
Mace ba ta finki
Nutsuwa gare ki
Hankali gare ki
[Verse 16]
Fara'a gare ki
Murmushi gare ki
Kin yi kyau abin ki
Kin ci zamaninki
Dole ne su ganki
Su yi ta kwaikwayonki
An fi son fadarki
[Verse 17]
Sai ku zo ku duka domin ku gaishe da Fatima 'yar lele
Shalele
Yaraye iye ayye yaraye iyeh
Sannu sarauniya Fatima ke ce adon gari 'yar lele
Written by: Ali Isah Jita

Shazam Footer

Select language:
Google Play Store
Apple App Store
Chrome Web Store
Galaxy Store

Follow Us

Loading...