album cover
Fansa
5,354
Pop
Fansa was released on March 17, 2020 by Amjad Records as a part of the album Fansa - Single
album cover
Release DateMarch 17, 2020
LabelAmjad Records
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM109

Music Video

Music Video

Credits

COMPOSITION & LYRICS
hamisu said yusuf
hamisu said yusuf
Songwriter

Lyrics

[Verse 1]
Ka yarda ina sonka a zuci da fili
Kuma ba domin fansa ba
Ba don ka iya zance ba
In dai ka aminta ni ce tauraruwarka ka ba ni dama
[Verse 2]
To ni ma ba zan karyata ƙauna ba
Ban ce ban san yarda ba
Ba don ɗaukar fansa ba
Amma na kasa gane cikinku wace jaruma
[Verse 3]
Juyo ka kalleni na yi adona duk a dominka ne
Kullum ina tantamar yaushe ne za ka karɓe ni ne
Ka ba ni dama don ka ga dukan sirrina na bayyane
Ka mance zan kai ka gida don gai da Abbanmu ne ma
[Verse 4]
Kina bayyanai ji nake tamkar ke ce ni zahirinki
Zuciyata sai in sa yarda da tunanin mallakinki
To amma wani sashina na ce min kar na biki
Don ban son ta da husuma
[Verse 5]
A duniyar nan babu wadda ta kai ni a soyayyarka
Kana kishinka
Kuma ba wata wadda nake jin zan iya kawo wa ajiyarka
Na ɓoyeka
Ni ban da buri a kullum wanda ya zarce in anbace ka
Sirri so ne haƙiƙar ƙauna ni nake bayyana ma
[Verse 6]
Ke ma kin bayyana naki nima dole in bayyana nau
Kan kin ce min ya sanki a zuciya sai in ce miki lau
To ki bini a sannu idan sa'ar ki ta cimmini zana bi nima
[Verse 7]
Dama ana buɗe zuci a kalla abin da da duk ke cikinta
Da ban da bakin in furta sai dai in aje a gabanka
Don Allah kai lamunin so ko da yini guda ne in ganka
Mai sonka shi za na so kana in dinga mai hidima (Midget mix)
[Verse 8]
Soyayyarki tana raina, kullum ɗaɗuwa take
In na farka bacci na, na ganinki zuwa yake
Amma duk da hakan na san soyayya sa'a ce
Don haka ba ni ba yarda
Written by: hamisu said yusuf
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...