Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Nazir M. Ahmad
Nazir M. Ahmad
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nazir M. Ahmad
Nazir M. Ahmad
Songwriter

Lyrics

[Verse 1]
Dan sahu
Da shi zan gida na yo aure (Dan sahu)
Da shi ne z ana so in karo wata (Dan sahu)
Da shi ba zan je bara ga kowa ba (Dan sahu)
Da shi ne zan taimakawa 'ya'yana (Dan sahu)
Da shi ne zan ba uwa da kannena (Dan sahu)
Da shi zan ci abinci har iyalaina (Dan sahu)
[Verse 2]
Da shi jama'a ke ganin mutunci na (Dan sahu)
Sana'ar da take ta daga sunana (Dan sahu)
Da shi ne nai wa talauci ban kwana (Dan sahu)
Da shi 'yan mata suke ta kallo na (Dan sahu)
Da shi na wuce gori ko a dangi na (Dan sahu)
Da shi nai kima cikin abokaina (Dan sahu)
[Verse 3]
Da shi naka daukar nauyin karatu na (Dan sahu)
Da shi ne aka min miya da kifi na (Dan sahu)
Da shi nai odar shayi da madara ta (Dan sahu)
Da shi na ci biredi har da dan kwaina, ka biya mu
[Verse 4]
Mu ga mu da dan sahunmu
Injin buga 'yan kudinmu
Sana'armu da 'yan uwanmu
Sana'armu da 'yan uwanmu
[Verse 5]
Ya tabbata 'yan garinmu
Darajarmu sana'o'inmu
Gandujenmu shi da kan shi yacce mu yi dan sahunmu
[Verse 6]
Mu ga mu da dan sahunmu
Mu ga mu da dan sahunmu
Injin buga 'yan kudinmu
Sana'armu da 'yan uwanmu
Sana'armu da 'yan uwanmu
[Verse 7]
Ya tabbata 'yan garinmu
Darajarmu sana'o'inmu
Gandujenmu shi da kan shi yacce mu yi dan sahunmu
[Verse 8]
Bana Ganduje ya zo kanmu
Ya tashi da tallafinmu
Ya ce mana don diyanmu
Ya soke haraji gunmu
[Verse 9]
Mu gwamnati ta biya mu
Mun dogara ne da kan mu
Mun kama sana'o'inmu
Mun tsaya da kafafuwanmu
Mun rungumi dan sahunmu
[Verse 10]
Allah rike hannuwanmu, Amin
[Verse 11]
Ku ce mun gode
Ka yi mana tallafinka ne Gandun aiki
Za mu yi maka tallafinmu sai ranar yaki
[Verse 12]
Na ce mun gode
Kanawa Ganduje yai rabon kayan aiki
Spare tire, injin oyel duk dai ya ba mu
Mun ce mun gode
Ya janye haraji wanda aka dora kanmu
[Verse 13]
Mu je maliya daji wanda ba a masa keji
Mu je zaki wanda ba a nuna masa gun ji
Jirgin kasa wanda ba a mai hanyar burji
Ka tabbata khadimin da ke son Islama
[Verse 14]
Ashe ka ci Ganduje
Ba sai an yi zabe ba
Ka bi ka kwashe
Ba sai an yi shara ba
[Verse 15]
Kana ta ka kana ta su
Abin dole da ban haushi
Bar su Ganduje ba sai an yi gaba ba
Ka ci Ganduje ba sai an yi zabe ba
Ka bi ka kwashe ba sai an yi shara ba
[Verse 16]
Kana ta ka kana ta su
Abin dole da ban haushi
Bar su Ganduje ba sai an yi gaba ba
[Verse 17]
Bar su Ganduje ba sai an yi gaba ba
Yanzu ta juya giwa na gudun kura
Yanzu mun san dabarun mai shirin kara
Mu kanawa da masu gudu muke tsara
Wasu sun tashi ga shi suna shirin kaura
[Verse 18]
Zabuwa dai da zanenta a gadon baya
Mai ya dame su ga shi muna ta linkaya
Duk tsawon zamaninka wadansu na baya
Ko ka yarda da Allah ko kace lala lala
Mu 'yan Kanon dabo Baba muke yi wa hidima
[Verse 19]
Ka ci Ganduje ba sai an yi zabe ba
Ka bi ka kwashe ba sai an yi shara ba
Kana ta ka kana ta su
Abin dole da ban haushi
Bar su Ganduje ba sai an yi gaba ba
Allah Ya sa mu dace Amin
Written by: Nazir M. Ahmad
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...