album cover
Idi Master
10,401
Blues
Idi Master was released on February 2, 2020 by Sarkin Waka Musical Studio as a part of the album Ana Tayi Muna Taji
album cover
Release DateFebruary 2, 2020
LabelSarkin Waka Musical Studio
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM67

Credits

PERFORMING ARTISTS
Nazir M Ahmad Sarkin Waka
Nazir M Ahmad Sarkin Waka
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nazir M. Ahmad
Nazir M. Ahmad
Songwriter

Lyrics

Zance a yi zance, a yi zance, a yi zance dai
Mu 'yan Nijar mun zo, yau 'yan Nijar mun zo
Zan ce zane ya zo, zan ce zane ya zo
Aka ce Idi Master karshen zance an zo
Karshen zance ya zo
Aka ce ma maliya sai suna yab bika
Aka ce ma zaki sai kan nemo harka
Aka ce ma tauraro sai haske yab bika
Aka ce ma giwa sai girman ka ɗauka
Aka ce ma gwamnati sai ka turo aiki
Aka ce ma mai ɗa'a sai kas samo sa'a
Aka ce ma banki sai kuɗɗi yai aiki
A ƙasar Nijar kai kaka ɗaukar ɗaukacin kirki
A ƙasar Nijar kai aka cewa namijin aiki
A ƙasar Nijar ka zama kwano mazubin kirki
A ƙasar Nijar kai aka cewa ba da mamaki
A ƙasar Nijar ba ka da wari a sa'anninka
A ƙasar Nijar kai ne mai motocin kirki
A ƙasar Nijar kai ka zamma Kwankwaso gun aiki
A ƙasar Nijar kai ne mai sarkin waƙa
A faɗa a cika wannan sai kai Idi Master
A yau ƙauyen ne birni
Ashe rami ne gulbi
Ɗan zaki ya girma, ɗan zaki ya girma
Iɗan kafa ta tsayu ganga ta kan kau da haka
Ashe a karshen magana ƙauyukan ne birni
Kun ga su damisa
Sai dai ƙwamusa
Alhaji Idi Mastern nan da ace kasa
Yau shi ne dai Allah ya aza bisa
A faɗa a cika, na ce ka faɗa ka cika
Kai ne haka iɗan kacce za ka yi
To za ka yi ba karya ba
A yau ƙauyen ne birni, a yau ƙauyen ne birni
Ashe rami ne gulbi, ashe rami ne gulbi
Ɗan zaki ya girma, ɗan zaki ya girma
Iɗan kafa ta tsayu ganga ta kan kau da haka
Ashe a karshen magana ƙauyukan ne birni
Kun ga su damisa (ashe)
Sai dai kwamusa (gaske)
Alhaji Idi Mastern nan da ace ƙasa
Yau shi ne dai Allah ya aza bisa
Ku ce Bismillah Allah, Bismillah
Ya Rahmanu jigo na Allah
Allah kai ka iya mana
Rabbi ka taimaki mai yin sallah
Ce mana Amin
Allah sa mu gama lafiya (Allah sa mu gama lafiya)
Kayyi salati ga Muhammadur Rasulullah
Wanda ya kawo sallah
Ahmadu baban Zahra
Sa da sahabbai da iyalai da masoya sallah
Ku buga min in waƙe wanda aka yi wa ni'ima
Ta 'ya'ya da kuɗaɗe da gidaje jimla
Na mutanen ƙauye har da mutanen birni
A yau ƙauyen ne birni, A yau ƙauyen ne birni
Ashe rami ne gulbi, rami ne gulbi
Ɗan zaki ya girma, ɗan zaki ya girma
Iɗan kafa ta tsayu ganga ta kan kau da haka
Ashe a babbar magana ƙauyukan ne birni
Ƙauyukan ne dai (Kun ga su damisa)
Uhm sai dai kwamusa
Uhm Alhaji Idi Mastern nan da ace kasa
Yau shi ne Allah ya aza bisa
Zance a yi zance, a yi zance, a yi zance dai
Yau 'yan Nijar mun zo, yau 'yan Nijar mun zo
Zan ce zane ya zo, zan ce zane ya zo
Aka ce Idi Master karshen zance an zo
Karshen zance ya zo
Aka ce ma maliya sai suna yab bika
Aka ce ma zaki sai kan nemo harka
Aka ce ma tauraro sai haske yab bika
Aka ce ma giwa sai girman ka ɗauka
Aka ce ma gwamnati sai ka turo aiki
Aka ce ma mai da'a sai kas samo sa'a
Aka ce ma banki sai kuddi yai aiki
A ƙasar Nijar kai kaka ɗaukar ɗaukacin kirki
A ƙasar Nijar kai aka cewa namijin aiki
A ƙasar Nijar ka zama kwano mazubin kirki
A ƙasar Nijar kai aka cewa ba da mamaki
A ƙasar Nijar ba ka da wari a sa'anninka
A ƙasar Nijar kai ne mai motocin kirki
A ƙasar Nijar kai ka zamma Kwankwaso gun aiki
A ƙasar Nijar kai ne mai sarkin waƙa
A faɗa a cika wannan sai kai Idi Master toh
Haji Idi Master ka bar su da mamaki
Haji Idi Master kai kak kawo taki
Haji Idi Master kai ne da yawan maki
Haji Idi Master kai ne dai sha raki
Zancenka zai shiga duniya don ka zama hamshaki
Haji Idi Master mun samo labari
Haji Idi Master kai ka zama alkhairi
Haji Idi Master kai ba ka nufin sharri
Tafiyarka a fannin sa'a sai kazzama limami
Haji Idi Master duk sun ja sun bar ka
Haji Idi Master kowa sai ya bi ka
Iska ka wuce duka zaki ba tamkarka
Tafi sannu sarakin da ake zo wa gaishe sa
Tafi sannu madi kai da tabi kai ka yi daidai Sir
A jikinka ado ya zama tamkar kai kai yi yo sa
Aka ce ma can Sir sai kai kaz zama kusa
Aka ce sarkin waƙa ni kuma sai nai waƙa
Muka ce ma somin tabi ce wannan waƙa
Waƙarka tana hanya alaji Idi Master
Allah Ya sa mu dace, Amin
Written by: Nazir M. Ahmad
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...