Credits
COMPOSITION & LYRICS
Ahmad Delta
Songwriter
Ahmad Idris
Songwriter
Lyrics
(Beat Amjad Record)
Da kallo guda jiki na da rai kin sace
Kalaman yabo idan za nayi su don kece
Ina jin yawan bugun zuciya ba sassauci
Ina son ki ko'ina zan fada a san kece
(Sai da kai)
Ina kasa cin abinci
Balle na iya bacci
Kullum ina maraici
Ke zaki debe kewa
Zan baki lokaci na
Kinyi dai-dai da ra'ayi na
In babu ke ina jaddadawa toh za'a ganni gawa
Mafarki nake, ina wai kike? Da zan gan ki
Akwai sakunan da nayi tanadi da zan baki
Kawai damuwar, ido so suke su kalle ki
Kina min gizo tsawon lokuta da surar ki
Kan so ina ta fama
Wa za naje na kama?
Ke zaki bani dama
In bar kishi da hamma
Bar shakka
Ban saka kiyi kuka
Da hakika
Alkawar na dauka
Ban barin ki, damina ko kaka
Kin yi shuka, inda za kiyi girba
Wayyo dan saurayi
Har ka ban tausayi
Ya za nayi?
Naji sauyin yanayi
So ya taba ni
Ya samin tunani
Bani magani
Ga hannu na ka jani
Inuwa ka kai ni
In samu suku ni
Yau taka ce ni
(Midget Mix)
Da kallo guda jiki na da rai kin sace
Kalaman yabo idan za nayi su don kece
Written by: Ahmad Delta Delta, Ahmad Idris