Lyrics
(Beat A1 Records)
Kalaman soyayya
Da kaunar ka nake kwana
Amfanin fitila haske
Da kaunar ki nake kwana, nake tashi
Ina so kiji tausayi na ko mun saba
Da kaunar ka nake kwana, nake tashi
Ina so kaji tausayi na ko mun saba
Idan zan fadi kalmomi na soyayya
Siffofin ki nake duba
Dake za nayi tarayya abar so na
Ba za nayi miki tamka ba
Babu diyar da nake kauna da ta kaiki
Ba za nayi miki karya ba
Masoyin ka kayi mai so, domin Allah
Koba Naira ba komai ai mun saba
Yau jirgin tafiya ya zo, mu mun cilla
Amfanin fitila haske
Don lada aka yin sallah, masoyi na
Dakai zana ci dan wake
Ka koya mini na saba, da soyayya
Sirrin zuci rike damke
Ko'a ina kai zan nuna, ina son ka
Bazan canza tunani ba ai mun saba
Ina son ka
Banga tare ba, turmi na gudun tabarya
Ban ki gaske ba, ba kai babu daura kaya
Banji zanyi ba, ha'inci a so da karya
Banyi kwance ba, mene zai hanani zarya
Bani tagumi, mai rai zai ishe maraya
Kai duniya, tunani nake na baya
So da alkawar, mu damke muje mu kurya
Babu lafiya ban gan ki a kusa na ba
Naji na gani, da kai zanyi rayuwata
Bani ba wani, sirrin zuci manufa ta
Zanyi gwangwoni, indai har kayi mini rata
Fitar gani, ido ka ciran makanta
Sani dariya, daure kayi mini gata
Kaini-kaini ni da kai zan wuce makwanta
Kara kyan gani, a so kar kamin mugunta
Nawa naka ne, bazan barka ko dare ba
Naso kiji tausayi na a soyayya, koda nayi miki laifi
Da kaunar ka nake kwana nake tashi, ka saurari kalamai na
Da kaunar ki nake kwana nake tashi
Ina so kaji tausayi na ko mun saba
Written by: SANI AHMAD


![Watch Sani Ahmad [ Kalaman Soyayya] official video 🥰😍💖 on YouTube Watch Sani Ahmad [ Kalaman Soyayya] official video 🥰😍💖 on YouTube](https://i.ytimg.com/vi/5U5ENZDiUUA/hqdefault.jpg)