Lyrics

Mai madi ka tallar zaki A'a toh shi kam mai zuma Gida ya ke zaune ne Ku ko malamai ku dauko littafanku Tunda dai kune ne manya Ku karanta ku fassara mana aya A yanzu dai shine dai dai Musulunci akwai nasiha a cikinsa Wanda kuma Allah ya so Manzon Allah yayi Amma yanzu mun ciro al'adunmu Masu son lalata mu Don yau ba a baka aure ba kudi Wai su sai so su baiwa Mai takama da adda a cikin gida Yana datse kannu Suna samun kudi Sanan zasu bashi mata kyakykyawa Gani ni kuma Babangida Ina so inyi aure Ina son auren diyan kabawa Babangida Ni kuma gani bani yin minti dai ruwa Ina son inyi aure Ina son auren badakkara ni Babangida Ni kuma gani ban da walki gindina Ina son inyi aure Ina son auren basakwkwata ni Babangida Sanan ni gani ba batoranke ne ba Ina son inyi aure Ina son auren diyan Fulani Babangida Ni kuma ga ni ban da shanu ba rugga Ina son inyi aure Ina son auren Bagobira yar Gobir Amma ni ba ni son ace bawa ne ni Ina son inyi aure Ina son auren Bazazzaga ni Babangida Ni kuma ba ni cin faten doya kullum Ina son inyi aure Ina son auren Babarbara ni Babangida Sissan nan na gwal ka sani ina sauna Ina son inyi aure Ina son auren Bakambara ni Babangida Ni kuma ga ni bani son daukar kaya Ina son inyi aure Ina son auren diyan Kanawa Babangida Ni kuma ga ni ban da tsagen baki Sannan ni ga ni ba gajere ne ni ba Ina son inyi aure Ina son auren Bakatsina ni Babangida Katsinawa na dikko dakin kara Kunya garesu ba dai tsoro ba Ina son auren Bakatsina ni Babangida Ni kuma ga ni bani son yaki ko kusa Ina son inyi aure Ina son auren Bazamfara ni Babangida Ita tana kaunata ni ina ra'ayinta Ubanta sai yacce a'a Ita tana kaunata ni ina kaunarta Ubanta sai yace "um-um" Wani da bata kauna Wai dashi za'ayi aure Toh don Allah a daina auren dole Saboda auren tilas Kasa diya yawon banza Ba wulakantance a yanzu sai marar ilmi Ko mai ilmi ku gane ya kece raini Ba wani mai yi mai Da sana'a Da fahimta Kowa da wadda Allah nayyo mai In sahiya ta waye Wadansu na aikin gona Wadansu suna office Wadansu karatu Wadansu ko waka sun kai Haka nan Allah yaso Tsuntsu asalin gidansu kan ice ne Kifi asalin gidansu bai wuce rafi ba A'a ni dai Babangida Duniya ko tai man kida bazan taka ba Du wanda ya taka yaga kwam Cin hakin sama sai rakumi Awaki kuci kasuwa Kuko kuyi hankuri Inda Allah bai kai mutum ba Qaqa zai kai can Akuya ba ta layya inga rago Du na Annabi Na tabbatar bazai lalace ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out