Credits

Lyrics

[Verse 1]
Eh! Mai kwalliyar jiki Zeena fara hasken idaniya
Rayuwa ta duniya sai hakuri kar ki duba zamani
[Verse 2]
Eh! Sai sannu-sannu don Zeenat ni na fara nazari
Rayuwa ta duniya sai hakuri na kyale zamani
[Verse 3]
Komai da lokaci Zeenatu suna wanda yai daban
Mai son ya yo fice yai hakuri zai zama adon gari
[Verse 4]
Eh! Kauna akwai ta yau za nanfado so ne ruwan jiki
Ki yi tankadenki Zeenatu ki dau gari ki bar tsaki
Bayanki na tsaya zana yi kuka in kina haki
Mugun ruko ake miki idanuna suna gani
[Verse 5]
Komai da lokaci Zeenatu suna wanda yai daban
Mai son ya yo fice yai hakuri zai zama adon gari
[Verse 6]
Eh! Yau ni a rayuwa na yi ganin sauyi na yanayi
Cuta ake ta yi min a gida ba yadda za na yi
Ba wanda za ya nunan kauna ya aje ni dausayi
Kuka na zuciya na daduwa don za su badda ni
[Verse 7]
Komai da lokaci Zeenatu suna wanda yai daban
Mai son ya yo fice yai hakuri zai zama adon gari
[Verse 8]
Eh! Duk wanda rabbi yai wa baiwa to za ya sha wuya
Hujja abar rika Zeenah kina fama da makiya
In kin ce jarrabawa gaba za ki zamo zinariya
Ni ina da tausayi na ki a rai ba yau ba tuntuni
[Verse 9]
Komai da lokaci Zeenatu suna wanda yai daban
Mai son ya yo fice yai hakuri zai zama adon gari
[Verse 10]
Komai da lokaci Zeenatu suna wanda yai daban
Mai son ya yo fice yai hakuri zai zama adon gari
[Verse 11]
Eh! 'Yar gata na tashi gun umma da abbana sun ban kula
Da akwai su rayuwata kuma waye za ya dagula
Ga shi na zamo kamar baiwa na rasa gu na dabdala
Mutuwa ta haddasa na rasa canjin mai kula da ni
[Verse 12]
Komai da lokaci Zeenatu suna wanda yai daban
Mai son ya yo fice yai hakuri zai zama adon gari
[Verse 13]
Eh! Taso ki dena kuka mana Zeenatu 'yar marainiya
In ranki ya yi daci daure ki tuno hawainiya
Girmanta kin ga ta yi shi iyaye babu duniya
Canjin kala take in ta fito sai an yi sansani
[Verse 14]
Komai da lokaci Zeenatu suna wanda yai daban
Mai son ya yo fice yai hakuri zai zama adon gari
[Verse 15]
Eh! Ka yi min zancen da yas san nutsuwa raina na sanyaya
Kai dai nake gani fuska fari ga 'yar manuniya
Maganar da ka yi min ta shiga kunne ga hatsaniya
Sarkinmu zai yi duban lamari sauki da tsanani
[Verse 16]
Komai da lokaci Zeenatu suna wanda yai daban
Mai son ya yo fice yai hakuri zai zama adon gari
[Verse 17]
Eh mai kwalliyar jiki Zeenah fara hasken idaniya
Rayuwa ta duniya sai hakuri kar ki duba zamani
[Verse 18]
Eh! Sai sannu-sannu don Zeenatu ni na kara nazari
Rayuwa ta duniya sai hakuri na kyale zamani
[Verse 19]
Komai da lokaci Zeenatu suna wanda yai daban
Mai son ya yo fice yai hakuri zai zama adon gari
Written by: Farouk M Inuwa, Isa Gombe, Mubarak Dutse, RR
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...