album cover
Halwa
7,854
R&B/Soul
Halwa was released on January 1, 2017 by Shareef Studios Invest Nig Ltd as a part of the album Babbar Yarinya
album cover
Release DateJanuary 1, 2017
LabelShareef Studios Invest Nig Ltd
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM

Music Video

Music Video

Credits

Lyrics

A cikin halwar soyayya nayi gamo, gamo mai alkhairi
A cikin halwar soyayya nayi gamo, da hasken annuri
Juma'ar da za tayi kyawo, tun daga labara ake iya gane ta
Tun farkon haduwar na gane, kunci zuciya zaki wanke ta
Domin natsuwa da kamalar ki, na gane a cikin su kin bambanta
Rabbi shi ya hada mu cikin kauna, ni da kai a sannu muka daidaita
Halayya ta da naka sukayi arba, sun zamo daya ba mai nufin cuta
Godiya ga rabbi kawai zanyi, da ya bani kai yayi min kyuta
A cikin halwar soyayya nayi gamo, gamo mai alkhairi
A cikin halwar soyayya nayi gamo, da hasken annuri
Auren mu na so in an kai daurawa
Sabuwar rayuwa mu komawa
Ayyukan gida zamu tarawa
Mu raba kowa yayi kamawa
In na nemo abinci na kawowa
Keko aikin kine kiyi girkawa
Tambura idan nayi dokawa
Wajibin ka waka rerawa
Da kalaman nan naka da dada
Masu sanyaya rai yayi kwantawa
Bakin jiki sutura in ka sanyawa
Mata in sun ganka dole suyi kyasawa
A cikin halwar soyayya nayi gamo, gamo mai alkhairi
A cikin halwar soyayya nayi gamo, da hasken annuri
Ba a bada rikon soyayya, wanda yayi banga dalili ba
Bada amana akan yarda ne, wanda yaci baiyi halacci ba
Tausayi silar soyayya, mara shi bazai yi mutunci ba
Gaskiya take sa ayi karko, koda hassada ba za'a rushe ba
Sammakon da nayi a soyayya, na tabbata banyi ta a iska ba
Nayi azarbabi wasu ke cewa, har yanzu banyi gamo da illa ba
A cikin halwar soyayya nayi gamo, gamo mai alkhairi
A cikin halwar soyayya nayi gamo, da hasken annuri
Nayi gamo, gamo mai alkhairi
Written by: Umar M Sharef
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...