album cover
Barewa
77
Pop
Barewa was released on June 8, 2018 by White House as a part of the album Mai Laya
album cover
Release DateJune 8, 2018
LabelWhite House
LanguageEnglish
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM157

Credits

Lyrics

Idaniya zubar ruwa
A zuciya tana ta demuwa
Wa zaya kauda da damuwa
Ya bani ruwa nasha
Ciwon jikin barewa a daji wazai bata kanwa?
Allan dayayi barewa, zai bata magani
Nace ki gyra kaya, bance mu raraba ba
A da a baya, nace kiyo hakan ba
Kin zagaya ta baya, kin je kinata kwaba
Ko nayi laifi, danace kije ki tuba
Duk wanda ke zagaki, bai zama adali ba
Kibi hanyar gaskiya, ba so na zuciya ba
Kul fa ki daina barna, dan kar akama jaba
Ki kama Allah, ki samu lamuni
Kina da kyau a fuska amma zuci babu haske
Kin bata garri, kwara guda na wanke
Kin kauce duka hanyar da zaki goma aike
Wazai yi aure da yar gidan kulake
Kullum dare da rana, ina ta sasake
Cikin mutane, sai dai in dinga yake
Ciwon dake a raina, ya za'ayo ya warke
Hakuri dake ashe shine magani
Nasoki a zuciyata, tun shekaru na baya
Tun kina karama kece masoyiya
Ina ta kafa, kafa da sanki babu karya
Ashe watan wata rana, zan sha bakar wuya
Kowa ya ganki zai ce kina da tarbiya
Fuskarki tai kama da masu gaskiya
Kince ni kadai ne a ranki gaskiya
Sai gashi kin bi hanyar, dadi na zamani
Keko madujala sak
Koko ince garaya
A kada ki a titi
Koko cikin mashaya
Kin tsallake uba har da uwa kin kama hanya
Kin zabi duniya tarbiyar ki babu kunya
Nazo na taimaka karshe sai ta juya baya
Da kyau na dan maciji gara kare dake biyaya
Shi dan hawainiya dole kace shi maraya
Shi ba kowa bane, sai ya biye wa zamani
Kina da zubin mutunci amma kin iya nuke murci
Kin sani sake, sake har na kasa cin abinci
Ni da zato da nai kauna ce ganin karamci
Ashe ko nayi gwari
Zango nai rashin azanci
Kira gadon iyaye wace muke mu samu abinci
Wani ko hana shi gadon nama bai zama abinci
Bawa a zamanin nan shike zama da kunci
Ni na godewa Allah
Nabar ku da zamani
Na samu 'ya ta kirki mai kyau har na kai sadaki
Ga asali a gunta, rayuwar ta nada sauki
Kuma ta iya kwalliya wanda yake saka ni dauki
Kaunarta a zuciya, gashi na fada da baki
Guna ta zam halali, makiya suna ta tsaki
Wasu nata tsegumi
Su jaba a tura baki
Allah ka tsare gidana da sharin diya na awaki
Ka bamu kariya, daga wanga zamani
Idaniya zubar ruwa
A zuciya tana ta demuwa
Wa zaya kauda da damuwa
Ya bani ruwa nasha
Ciwon jikin barewa a daji wazai bata kanwa?
Allan dayayi barewa, zai bata magani
Written by: Adam. A. Zango
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...