Lyrics

Kura daban da kora Dauri daban da dauri Amma wurin rubutu kalmomin na kama da juna Waka kwarai sani ce Tsarata hikima ce Rerata ba azanci Kowa bazayi tabbaci ba Malam yana bayani Yara ku jini Mai hikima kadai zaya kwance kullin zaren batuna Kai gafara mazaga shago Garan zuma da kura kogo Mai hakurin kadan na tabbata ba zai zaman rashi ba Mai dogaro ga Allah wannan ba'ayi babu shi ba Kai de ka kara hakuri Daure ka kara jumuri Bawa ka rike guzuri Kyakkyawan gamo ga Allah shine babban rufin asiri In kaci naci, kasha nasha malam dame kafini Toh gani na fito namiji ba mai tareni sai goga In kaji ka iya toh ga wuri muja daga Tsoron gamo da Allah dai nake (Ka gama kalau lahiya) Ni dai wannan zai sani in sake (Sarkin waka gonar waka) Ba yau nake tunaniba Ba yanzu mai wucewa ba Ban san abinda zai faru gobe ko anjima gabana ba In kaji kida murna ce Ba'a tambari kuka ba Fadar ina dashi rubace Matsoraci bazai suna ba Ku bar ganin mutun kaskance Ba tabbacin ba zai shura ba In Rabbi yai nufin karuwa sai ta rigaka samun tsira Nemi lahira bawa dan duniyarga ta zama saura Aje abun fada mai kyau ranar da babu kai ka tsira Daukaka nufin Allah ce Rabbi in yaso kai dace Gwani ya ganin dan koyo Zai fishi nasara ko suna Kar ka damu kar kaji tsoro Duk cikar wuri duk taro Nuna asalinka da shenki zai baka nasara wataran Natsu kawai ka nemi na kanka Dan yanzu babu mai taba baka Kai hakuri wajen nemanka zai baka arziki watarana Farincikin marar shi mai shi ne Mai shi farincikin shi marar shi ne dole a rayu bangon juna Sirrinka ya zaki sirrinka Kar ka yawaita nuna kalarka Maganin dukan matsalarka lillahi zaka kaiwa kuka Ubangiji ina rokonka ba dan isa ba ko matsayina Rabbi yafe duka kuri na Martabar fiyayyen bayi Rabbi yafe duka kurina Martabar fiyayyan bayi Rabbi yafe duka kurina Martabar fiyayyen bayi
Writer(s): Tasiu Abdullahi Unguwa Uku Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out