Lyrics

Ni fah mun dace da kai Babu ni in babu kai Mallaki ce ni da kai (Abbah ce Beats) Ni fah son ki ya mamaye ni A kan ki wasu kuma sun tsangwame ni Don na rike ki tsani gare ni Kan ki nasan zan taka tsani Ba abinda zai gagare ni Kece guda tilo nayi nuni Yarda ayi mana baiko Gidan ku manya na aiko Da ke na hau zana sauko Kece mataki na farko Da zana bai wa soyayya Kina da kyawun halayya Farar diya mai tarbiyya Kina da dadin tarayya Zo matso kusa kar kiyi nesa In babu ke komai zana kasa Fushi a kan ki sam ba nayo sa Don Allah aure na kar ki fasa Ko da kina kusa ko kinyi nesa A zuci muna tare Da kai na fara zan kare Masu bakin ciki na kore Zama da kai ne zan more Duk kunnuwana na hure A kan ka ban ji bani gani Allah ya kauda maki gani Mai kin ka ban ma so na gani Kai ne ido na dake gani Kai daya tamkar ya sansani In babu kai ai babu wani Zan kai ma umma na ta gani Nayi sa'a na taka tsani A garen da kazam majnuni Ga ka mene zai gagare ni? Cikin su mata ba wadda ta kai ni Dole a ganni kuma haka a barni Ka ga son ka ya mamaye ni Koda yaushe muna tare Koda yaushe muna tare Kiji kece lissafi na Ma'aji na dukan sirri na Ki yarda kin zama mai daki na Yan'uwan ki su zama dangi na Dake kadai zan zauna Bani so ki guje ni Nasan kina da amana Duk inda zaki kija ni Farin masoyi, farin gani Fanni na kyau ga ka ba wani Kai ne kake bani magani In nayi kishi ka shayar dani Kula dani, kar ka yada ni Ga ka ba mai cutar dani Zan so a gan mu dake tare Dani dake bama ware Zugar magauta duka share Gida na auren mu ayi jere Na zam amarya kai ka zama ango Zaman mu ya rai daure (Alhaji Abbah ce on the mix)
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out