album cover
Kauna
17,360
Afro-Beat
Kauna was released on June 13, 2023 by Auta Mg Boy as a part of the album Kauna - Single
album cover
Release DateJune 13, 2023
LabelAuta Mg Boy
LanguageEnglish
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM130

Credits

PERFORMING ARTISTS
Auta Mg Boy
Auta Mg Boy
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Abdulrahman Muhammad Garba
Abdulrahman Muhammad Garba
Songwriter

Lyrics

[Intro]
Ƙauna garkuwan jiki, naki ya taɓa ni
Ke ce farin cikin raina, raina
[Verse 1]
Ƙauna garkuwan jiki, naka ya taɓa ni
Kai ne farin cikin raina, raina
[Verse 2]
So rayuwa ne wanda ke gini
Naki kin ka ba ni ya zamo sani
Zuciya da ruhi can kika yi rini
Ba kamar ki tabbas naji na gani
So ruwan zuma ne, kin yi min tuni ne
Za ni ba ki yarda ke ko ki bani ƙauna
[Verse 3]
Na yi farin ciki da soyayya
In na gan ka har ina kunya
Kar ka bar ni za na yo jinya
Maƙiya mu sa su su yi kunya
Kai ka ba ni ƙauna, na yi farin ciki
Rayuwarmu ta kasan ce da martaba
[Verse 4]
Yadda kika yi mini na godewa
Ƙaunar da nake maka nayi ninkawa
Shi ne sirrin da nake boyewa
Ko da ba ka furta ba ina ganewa
In dai kika ce min "kule" zan cashewa
To zo mu yi gasa aga mai sarewa
Ai kuwa ki shirya wa kafan tserewa
A gani a kasa tunda muna nan gamu
[Verse 5]
Babu kamarki duk cikin duniya
Ko da ganinki doguwar yarinya
Zama da ke kawai na shirya
Kyawun halinki ga ki mai tarbiyya
Mai farin idanu
Na yi ta jiran ki sannu
Zuciyarki tawa ce ai dole in kulawa
Dole na yi kulawa
[Verse 6]
Ka yi kira na amsa masoyina
Son ka yake mini yawo a ƙirjina
Ko jiya ma na ganka a barcina
Na yi ta fadin sunanka a bakina
Wata ta raɓe ka akwai ƙuna
Ni ɗaya ce ba ƙari da mun aure
[Outro]
Ƙauna garkuwan jiki naki ya taɓa ni
Ke ce farin cikin raina, raina
Written by: Abdulrahman Muhammad Garba
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...