Lyrics
(J Shareef on the beat)
Daga Allah ne
Ba yin mu bane ba
Ikon Allah
Nasarar bamu soma ma ba
Daga Allah ne
Ba yin mu bane ba
Ikon Allah
Nasarar bamu soma ma ba
(Daga Allah ne)
(Ikon Allah ne)
(Daga Allah ne)
(Nasarar bamu soma ma ba)
Allah yayi muma muna kan hanyar mu
Zamu je ga matakin mu
Allah ka bamu a hannun mu
Ba zamu taba faduwa a kasa ba
Allah ka duba mu
Ba zamu je inda za'a raina mu ba
Darajar mu da da'a gun mu
Ilahu ka bamu ka kara mana
Arziki da wadatar mu
Nema nake daga Allah ne
Tuba nake daga ne
Rayuwa nake daga Allah ne
Daukaka nake daga Allah ne
Daga Allah ne
Daga Allah ne
Mu tsaftace harshe kar mu bari
Girman kai yayi tasiri
Duk abinda ka shuka shi zaka girba
Dan uwa kayi nazari
Mu dai baiwar waka Allah ne ya bamu
Kuma bama fahari
Alkalami a saman takarda
Shi muka rike ya zam mana jari
Ga addu'a ta iyaye tana ta bin mu
A tun farkon fari
Hasbunallahu munka rike
Shiyasa muka tsallake duk wani sharri
Bawai iyawar mu bace
Koko kwarewa duk daga Allah ne
Daga Allah ne
A Baba ne (Daraja ne)
A Baba ne yaron nan
Waka nake, waka muke
Waka nake da fasahar nan
Li'ilafi ce, li'ilafi ce
Li'ilafi ce ke aikin nan
Zanyi zan gama kuma lafiya
Ba wani shegen man
Zanyi zan gama kuma lafiya
Da ikon Allah nan
Za mu yi nasara daga Allah ne
(Daga Allah ne)
(Ikon Allah ne)
Idan na tuna a lokacin dana fara
Anai min dariya
Anan na tsaya nayi nazari
Sannan kuma na karo idea
Na toshe kunnuwa zagi, hantara
Sai dai nayi dariya
Shawarar mama ma ta karfafe ni
Da nayi turjiya
A kwana a tashi ina tayi
Gashi Allah yayi min kariya
Har bana tantance adadin
Masoya harma da makiya
Allah ka kara tsare mu
Ka kara kulawa damu duk runtsi da wuya
(J Shareef Record)
Written by: Daraja One


