Lyrics
(Heavy music studio)
Yarinya, dan Allah muyi soyayya
Kice dani kin shirya
Dani zaki goggaya
Ko da yaushe ni din ne dai
Wanda ke son ki din ne dai
Mai yawon yabon ki akan dai-dai
Wanda zuciyar sa ta karkata dai
Na mace akan soyayyar ki (soyayar ki)
Bani jin kira sai dai naki (sai naki)
Bani tuna komai idan har baki
Koh ganin ido na yana shedar ki
Zana amsa koh wani suna naki (suna)
Idan kin min umarni ba zance naki
Cikin gidan ki daure ki maidan' sarki
Wanda zai kula da dukkanin al'amuran ki
Mai bada shawara a cikin fadar ki
Mai bada shawara a cikin dangin ki
Masoyiya ta kece (kece)
Ahh, kece
Zuciya tana son mai kyautata mata
Koh yaya yake
Wanda bai gudun ta dadi da wuya
Yana a nan inda take
Dan Allah ki zama abokiyar shawara
Hannu kar ki sake
In na shiga kuncin rayuwa
Sai ki bani guri na fake
Ko da tai nisa zuciya
Billahi baza ta guje ki ba
Baza ta manta ki ba
Hakkin ki bazai bari ta huta ba
Ahh, ahh, ahh
Ahh, ahh, ahh
Uhmm, uhmm, uhmm
Uhmm, humm, humm
Written by: abdulkadir tajuddeen


