album cover
Kyakkyawa
472
Music
Kyakkyawa was released on June 14, 2024 by Larabeey as a part of the album Kyakkyawa - Single
album cover
Release DateJune 14, 2024
LabelLarabeey
LanguageEnglish
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM89

Credits

PERFORMING ARTISTS
Larabeey
Larabeey
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Muhammad Saminu Aliyu
Muhammad Saminu Aliyu
Lyrics

Lyrics

Yauwa Yauwa yauwaa
Larabeey
Is Starcee The Magic Beats
Aci Gaba
Kyakkyawa Ke Kadai Zan Yi Wa Kirari
Da Kinji Dauki Wayar Ki Ki Kirani
Ranar Da Babu Ke Za'a Kai Ni Rami
In Dai A Kanki Ne Sai In Badda Jari
Farko Haske Na Gano
Wai Ashe Ma Ke Na Gani
Hasken Ki Yana Haska Min Zuciya
Kece Cuta Kece Magani
Dan Allah Zauna Kiji
Kalmar Da Banso In Ji Kalmar Rabuwa
Kin Tafi Da Rai Da Zuciya Da Gangan Jiki
Mai Kyawun Hali Kyawun Fata Da Kyawun Jiki
Zan Kula Dake Soyayya Ko Da Zan Ji Jiki
Na Kamu Da Soyayyar Ki Tun Ina Jinjiri
Bani Kula Sauran Mata Ni Naki Ne Ke Dai
Kanki Zan Ba Da Jini Na Gangar Jiki Har Rai
In Dai Kika Nuna Min So Ni Kan Ki Zan Komai
Zan Dinga Tarairayan Ki Ne Kamar Danyen Kwai
Dan Kin Hadu Ne Ga Diri Ga Kyau Ga Idanuwa
Ni Na Kamu Da Soyayya Mai Cike Da Damuwa
Burin Zuciya Na Ki Zame Mata Abokiyar Rayuwa
Da Kinyi Hakan Zaki Yaye Kunci Da Damuwa
Ina Zan Sa Kaina In Kika Bar Sashe Na
Ke Ce Zabi Na Ma'ajin Sirri Na
Ni Dai Na Lura Kece Ruhi Na
Kyakkyawa Ki Gane Ni Mai Son Ki Ne
Zan So Ki Ji Ni
Saurare Ni
Soyayyar Ki Ta Hanan Sukuni
Ki Tallafe Ni
Agaje Ni
Zuciyar Ki Za Ni Ba Ni Tsani
Sai Da Ke Zan Rayu Ke Ma Kinsan Haka Ne
Ba Wata A Zuciya Ta Duka Naki Ne
Wai Yaushe Za'a Ce In Turo Gidan Ku Ne
Ki Zam Amarya A Guri Na In Zam Angon Ki Ni
Tattabara Uwar Alkawari Na Samo
Ko Da Na Tafi Na Barki Sai Na Dawo
Kullum Zan Rika Nuna Miki Kauna Sabo
Dan ke Zantukan Soyayya Na Tsaro
Idan Na Barki Ina Zani
Saidai A Kaini A Shuka Ni
Soyayya Ta Kama Ni
Kyakkyawa Ta Zo Ga Ni
(Idan Na Barki Ina Zani
Saidai A Kaini A Shuka Ni
Soyayya Ta Kama Ni
Kyakkyawa Ta Zo Ga Ni)
Written by: Muhammad Saminu Aliyu
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...