album cover
Gaskiya 2
album cover
Gaskiya 2 was released on October 24, 2022 by Ahmad Shanawa as a part of the album Gaskiya 2 - Single
October 24, 2022
LabelAhmad Shanawa
BPM
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy

Lyrics

Gaskiya tana da zaki
Gaskiya tana da daci
Banje makaranta mai tsada bah
Banje Dubai koma banje London bah
Gaskiya tana da zaki
Gaskiya tana da daci
Banje makaranta mai tsada bah
Banje Dubai koma banje London bah
Kasheepun kida, okay
Beat amjad record
Wayyo na mutu yau na lalace
Shanawa kar kace dani baka so nah
Wanan da kaga mai kunu da kosai
Bani bace, ka karbi uzuri nah
Ina sonka ina kaunarka, nan da kwanaki kadan zamuyo gamo da juna
Ya zaki ce dani bake bace, bayan gashi nan na gano ki da idona
Bude WhatsApp ki sha kallo yanzu, ga hotunan dana dauke ki da wayana
Bani son kice dani nai miki karya, tunda kin gani dai ban saba ba
Ashe gaskiya tana da zaki
Ashe gaskiya tana da daci
Ashe gaskiya tana da rana
Makaryaci baza yayai dace bah
Tace dani yar aikin gidansu ce, sunanta salma sunyi shakuwa da juna ne
Hotonta shi take sakawa shafinta, chatting daga gidansu an hanata ne
Tace dani nazam jinin jikinta ne
Toh wai yaya batun zuwa Abuja ne
Nazo garin Abuja don mu warware, matsalar da aka samu ta binta ne
Idan na sauka a garin Abuja, Asokoro sunan anguwan su ne
Tace idan nazo AYA, in kirata zata zo ta same ni
Da ita da kawayen ta, amal da sufee su 'ya'ya manyan kasar mu ne
A nan mukai maganganu da ita sosai
Har muka sanya ranar zuwa Abuja
Gaskiya tana da zaki
Gaskiya tana da daci
Banje makaranta mai tsada bah
Banje Dubai koma banje London bah
A kwan a tashi ranar tazo, sai gani nan a hanya ta zuwa garin Abuja
Motar haya a ranar na shiga, direba ya saka mana wakar ado gwanja
Tafiyar awa kadan mukayai ashe, bacci ya dauke ni har idanuwa sukai ja
Direba sai yace damu mu sauka a maraba, shi baya shiga garin Abuja
A nan mukai tayi dashi ya karasa, damu cikin gari yace damu bazaya je ba
Ashe gaskiya tana da zaki
Ashe gaskiya tana da daci
Ashe gaskiya tana da rana
Makaryaci baza yayai dace bah
Na kira wayarta, ta daga nace na shigo abuja gani inda ta kwantanta
Tace na samu gu na dan fake, gasu nan zuwa da ita da kawayen ta
Kusan awa biyar na kai ina jiranta
Lambarta bai shiga, ah ta kashe wayarta
Sai ji nake kamar in fashe da kuka
A nan ta tabbata lalai nai wauta
Gashi nan dare ya fara shiga, na fara ma tinanin a ina ne zan kwanta
Tabdi jam, akwai babbar matsala
Written by: Ahmad Shanawa
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...