album cover
Hakkin So
77,047
Afro-Beat
Hakkin So was released on October 26, 2024 by ArewaBlog Records as a part of the album Hakkin So - Single
album cover
Release DateOctober 26, 2024
LabelArewaBlog Records
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM106

Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Salim Smart
Salim Smart
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Salim Smart
Salim Smart
Lyrics
Tsohuwar Ajiya
Tsohuwar Ajiya
Composer
PRODUCTION & ENGINEERING
Rakiya MOUSSA POUSSI
Rakiya MOUSSA POUSSI
Producer

Lyrics

[Verse 1]
Salim smart on the beat
Ahh, ba kowa zai gane ba
Yanda ake jin zugi
In dai har so ya ɗarsu
Ko kuma yai maka ɓarna
Ni kam so yai mini ɓarna
Ya canja min suffana
Ya mai san tamkar bare a cikin dangina
Ya sauyan lissafina
Ya tauye mini haƙƙina
Ya sa na baje sirrina
[Verse 2]
Sumbatun soyayya shin mene ne ke jawowa
Yaudara ce ko kuma kula ku ban amsata
Amma wani sa'in zuciyata ce ke harbawa
In na tuna cewa a soyayya na yo bauta
Wasu har sun canja mini kallona
Sun kasa su gano me ke damuna
Ni ɗai na san mene ne ciwona
Magani nasa Allah ɗai ne gatana
[Verse 3]
Ehh, in na mutu kai ne sanadi
Sannan kuma ba ka da madadi
Samun mace mai ƙaunar ka kamar ni ba lallai ba
Hanyar da ka nunan za na bi
A silar so nai maka ladabi
Amma haka bai sanya ka tunanin fasa butulci ba
Mene ne soyayya in ba ƙarya ce ba
Mene ne soyayya in ba cuta ce ba
Mene ne soyayya in ba haɗari ce ba
Na daina na huta har ƙarshen rayina
[Verse 4]
Yaya za ka yi da haƙƙin soyayyata
Ka saba mini da so kuma kai mun ƙeta
Ka bar ni alaƙa tamu ka yanke ta
Ka mamaye sashin zuciya ka canja ta
Ko wani laifi na yi ma ni ban roki ka yafe min ba
Domin na horu da soyayyarka tun ban saba ba
Yau kuka, gobe kuka, ni dai ba zan jure ba
Tun da Allah na nan adduʼa ce za ta yi gadi na
Written by: Salim Sadik, Salim Smart, Tsohuwar Ajiya
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...