album cover
Jatau
2,079
Afro-Beat
Jatau was released on January 1, 2024 by Taskata Global Services as a part of the album Sharafi Album
album cover
Release DateJanuary 1, 2024
LabelTaskata Global Services
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM120

Credits

PERFORMING ARTISTS
Adam. A. Zango
Adam. A. Zango
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Adam. A. Zango
Adam. A. Zango
Composer

Lyrics

Wayyo wayyo kai wannan zamani
Wayyo wayyo kai wannan zamani
Iyayen zamani
Matasan zamani
'Yan matan zamani
'Yan siyasan zamani
Malaman zamani
Masu kudin zamani
'Yan film din zamani
Har ma da mawakan zamani
Ku bude kunne kuji wakar jatau mai magani
Ni ne likitan zamani
Mai warkar da cutar zamani
Jatau (mmm)
Wayyo (mmm)
Mmm
Wayyo (mmm)
Allah mai zamani kuma shine zai mana magani
Allah yayi zamani toh a daina zagin zamani
Rami rami na shiga
Ramin kura na shiga
Ramin damusa na shiga
Ramin kura na shiga
Ramin alade na shiga
Ramin jaki na shiga
Ramin zaki na shiga amma zaki bai barni ba
Mmm
Wayyo (mmm)
Wayyo (mmm)
Ramin kura na shiga labarin sai ku tsaya kuji
Mutuwar aure ga hausawanmu abun har na gaji
Ina yin rangaji malamai akawo agaji
Dangi-dangi na shiga babu dangin da babu bazawara
Anyo aure na zuminci jama'a auren ya rabu
Anyo auren soyayya jama'a auren ya rabu
Anyo aure na dukiya jama'a auren ya rabu
Anyo aure na kiyayya Jama'a auren ya rabu
Jama'a kubiyoni jatau yau zani baku magani
Ilimin mata magani tarbiyar mace magani koda namijin baiyi shi ba
Wayyo (mmm)
Wayyo (mmm)
Malamanmu na zamani sai mu juya kallon zahiri
Dan wancan kungiya yacewa wancen kafiri
Shima dan kunyancan yacewa wancan kafiri
Toh wai wa zamu bi ku fada mana kar mu tsaya jiri
Musulunci guda ce ba banbanci a zahiri
Jatau mai magani ku biyoni zan baku magani cutar mata
Manzon Allah annabi shine zamu bi
Qur'ani kalmar Allah littafi zamu bi
Wayyo (mmm)
Wayyo (mmm)
'Yan siyasar zamani kuyi koyi da rukon gaskiya
Talakawan zamani sun zabe ku zuciya daya
Sai kuyi adalci in kun hau ku rike su da gaskiya
Kar ku manta sai da talaka mulkinku zai tafiya
In kau babu talaka mulkinku zai sunkiya
Wayyo (mmm)
Wayyo (mmm)
Wannan
Wannan
Wannan kai zamani
Allah ka tsare mana zamani
Karya wannan zamani
Hassada wannan zamani
Gulma wannan zamani
Cuta wannan zamani
Sata wannan zamani
Yaudara wannan zamani Allah ka tsare mana zamani
Mmm Allah ka tsare mana zamani
Jatau nine jatau mai magani
Jatau ni na baku magani
Wayyo (mmm)
Wayyo (mmm)
Wayyo (mmm)
Wayyo (mmm)
Written by: Adam. A. Zango
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...