Music Video
Music Video
Credits
PERFORMING ARTISTS
Umar M Shareef
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Umar M Shareef
Composer
Lyrics
Daga ke, daga ke, daga ke
Daga ke
Daga ke (amarya)
Daga ke
Daga ke ango ya rufe kofa
Daga ke
Daga ke ango baya yin kari
Daga ke
Daga ke ango ya rufe kofa (amarya)
(M. Shareefi)
Taso-taso amarya taso-taso
Taso ki fito ganin ki kowa ke so
Don ke muka zo mu nuna soyayya
Dangi da kawaye dukka baki daya
Ba wanda ya kai ki gun shigar kaya
Kyawun ki ya sa wadansu ke buya
A kyawu
A kyawu (amarya ba irin ki)
A tsafta
A tsafta (amarya ba irin ki)
A ilimi, karatu (amarya ba irin ki)
Biyayya, tarbiyya (amarya ba irin ki)
Daga ke
Daga ke karshe an ya rufe kofa (amarya)
Daga ke
Daga ke ango ya rufe kofa (amarya)
Daga ke
Daga ke yace baya yin kari (amarya)
Daga ke
Daga ke ango ya rufe kofa (amarya)
Sannu yar lalle
Sannu sha lalle
Marhabun lalle
Daga ke an kulle
Kece ya gano
Har ya dano tarko amarya
Zo shiga daki ya gino miki amarya
Da kin shiga zai yada makulin shi amarya
Don baya gani, bai jin zancen su amarya
Amarya ba kamar a gurin shi sam-sam
Zai rike ki da amana kam-kam
Da ci da sha abincin ki dam-dam
Dakin auren ki zauna daram dam
Kyakkyawa mai farin idanu
Yar cas-cas mai kyawun kamannu
Wayayya mai ilimin dukkan fannu
Ka dace ango nai maka sannu
Amaryar mu gimbiya
Amarya sarauniya
Amarya zinariya
Amarya taurariya
Ango na ta dariya
Ya more a duniya
Nasan baya shan wuya
Domin ke aminiya
Amaryar tamu ta hadu
Angon namu ya hadu
Kuma dukka kun hadu
Nima ai na hadu
Yar gatan umman ta
Yar gatan abban ta
Yar gatan dangin ta
Dukka suna son ta
Yau ta tafi dakin ta
Tayi ibadar ta
Ta zamto mata
Gata da angon ta
Duba idanun ta
Cike da murnar ta
Ta cika burin ta
An bata zabin ta
Shine ribar ta
Tayi biyayyar ta
Shine hanyar ta
Na shiga aljannar ta
Written by: Umar M Shareef