DAN ACHABA
511
Dance
DAN ACHABA was released on December 19, 2025 by Africori as a part of the album BEST OF ADO GWANJA VOL. 1
Credits
PERFORMING ARTISTS
Ado Gwanja
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ado Gwanja
Songwriter
Lyrics
Dan achaba
Rigarka bata sallah daga baya
Taka birki
Waishi kake da gaya inji mata
Dan achaba
Rigarka bata sallah daga baya
Taka birki
Waishi kake da gaya inji mata
In ka zarta toh dole za'a bika
In ka duka abinka za'a dauka
In ka birge tilas ayo yabonka
In ka bata wadansu zasu ki ka
Me yasan mata ka tsokanar ka
Halak ka dauka
Haramiya ka yada shi a baya
Kusan dalili kafin ku tambayi
Dan nai achaba
Tunkan na taka tsagi
Ya zanki nuni a sanda zaku ji ni
Maza da mata a sanu sai ku bi
Idan na kauce toh bani so kubar ni
Da ban aje ba
Wa zayace nazo muyi musaya
Eh zamu furta ko basu so mu rera
In guda yaki goma zasu dora
Bamu kyamar muyi kuskure a gyra
Mai masoya ai bashi yin gadara
Wasu ke ji da kansu suyi fitsara
Ga misali kafin na baku sai ku tuna baya
Wasu sunce mata muke wa waka
To uwa uba ne ai sai dasu a harka
A sanda mukai su sunka fara dauka
Da munyi waka su sunka nuna barka
Har ta dan achaban
Dasu naso na dauka
Su sunka yin ta
Na bita har na doka mata kwarya
Kai masaki dauko zare ka tafka
Kowa da faninsa ga inda kai ka dauka
Ado na Gwanja na zabi naita waka
Gata dan achaba wace nayi kuzo ku dauka
Mai yin sana'a cikin ruwa da iska
Neman halalinka kake
Ya zan na kwaye maka baya
Ni dai a guna ba kila ko wakala
Rigarka nace kasata kayi salla
Gaban da bayan rigarka baida ila
Wakar ka mata san ransu sunka kula
Dan suyi nishadi suyo rawa su shila
Shine na bisu
Amma a yanzu na waiwaye baya
Kai
Dan achaba
Rigarka zata salla ba karya
Mai bayyani
Adon gidansu Gwanja daga baya
Written by: Lericx Arewajams Dice

