album cover
Angara So
2,855
World
Angara So was released on May 10, 2018 by Apple Media Africa as a part of the album Iconic Sounds of Africa, Vol. 68
album cover
Release DateMay 10, 2018
LabelApple Media Africa
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM114

Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Hamisu Breaker
Hamisu Breaker
Performer
COMPOSITION & LYRICS
hamisu said yusuf
hamisu said yusuf
Composer, Lyrics

Lyrics

Da so yana rike amana ai bazai gujan ba
Don na rike shi hanu biyu yanzu yayai min zanba
Na kasa gane wanene ni akanki duba
Kauna saka hawaye ne nata raunin gunba
Na dauki agaran soyayya bazan gudu ba
In so zakayi dan Allah zaka samu riba
Idan na tashi bacci na ke nake tinawa
Gani nake kawai kece zaki ban kulawa
Bana tino dake zaki gujeni ban shiri ba
Na daura damarar soyayyarki ban cire ba
Hakan ya baki damar da kisani a ukuba
Da damuwa cikin ruhinawa ban cire ba
Basan abinda zai sanya yanzu ta fice ba
In na rufe ido na hotonki ke nuna min
Na kara angula sai nazari ya tabbatar min
Idan na tina irin san da nai miki da me yayi min?
Ina tana cikin ruhi haka yake tina min
Yanzun nagane cewa so ne bazan kuma ba
Shin me nai miki kika gwara kaina a jikin garu
A lokacin da kika shaida jamma'a sun taru
Kowa yanata kallona ni kuma ta faru
Ga zuciya tana ta rayan cewa na kwaru
Kaunarki tasaka ni naje samu miki faru
Amma hakan ga bai sa kin mini adalci ba
Idan na ganki kin damu hakan na damu na
Sai inta tausayi naki ki zauna gefe na
Na shaida haka nan sone na rike ki amana
Koda baki tinowa ba haka bai damu na
Don nai zama dake so bai sa na yinkure ba
Mutan garin mu nai mini shewa suna ta cewa
Wai so yanata dibana nayi haukacewa
Na damu da rike soyayyar ki ban gazawa
Idan na soki aganina nayi shalakewa
Ashe roko na gani nazataki sai na duba
Farin cikin masoyi ne ya samu mai bidar sa
Idan ya samu mai sansa kuma cikar burinsa
Ta zamto mallaki nasa hakan yasa a ransa
Idan sukayi aure a ganin su babu kinsa
Kawai su more shagalin su haka rai ya kunsa
Domin sun sa a rai ba wani wanda zai raba
Nasan akwai mutum daya wanda sukai mantawa
Munafikin da shi kullum yaga an watsewa
Shine burinsa rai nasa yaketa farantawa
Ya manta zuciyar wasu ne yake yin batawa
Nasan zaku tina soyayya na rushewa
Amma silarta wanan ne in kai kirgawa
Ga shawarata in yazo kar kuyi masa tarba
Nasan da kin tino da abinda nake son cewa
Amma koh kin tina ba amfanin ki rikewa
A yanzu banda burin da kizo muyi zaunawa
Nasan zakiyi hawaye wata ran kan ki macewa
Domin kin cuci ruhina rabbi zai sakawa
Ke kin saka hawaye igiya yana zubowa
A lokacin na dauka da ni zanyi macewa
Domin ina tinanin bake bazan iya ba
Kurman dare makaho ai ni nake zamowa
Idan dare yayi bacci nawa ban iyawa
Sanan idan gari ya waye bana fitowa
Amma akwai dalili daya wanda ke sakawa
Na kara so cikin jamma'a har muyai gaisawa
Wai me kike nufi san da kika ta fadan cewa
Dani dake takalmin kaza babu cirewa
Har alkawar kikai min wai zaki bani kulawa
Ashe burin ki daman dake inyi amincewa
Sanan sai ki sakamin rigar da ba cirewa
Rigar farar kaya wanda ciki taka sokewa
Amma ganin ido kyau a zubinta ba kushewa
Ashe diyar macici na rike kamar zuma
Yabon ta da nakeyi kullum babu irinta
Don kwaliyyarta in nagani na karan santa
Idan na kalla hanu nata koko kafafunta
Sai in ga tayi zanen kunshi yabi jikin ta
Hakan yake sakawa in ji nayo shaukanta
Ashe zata kujen san da taso tasa a rai
Written by: hamisu said yusuf
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...