album cover
Talaka
187
World
Talaka was released on April 17, 2018 by Apple Media Africa as a part of the album Iconic Sounds of Africa, Vol. 53 - Single
album cover
Release DateApril 17, 2018
LabelApple Media Africa
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM129

Credits

PERFORMING ARTISTS
Babangida Kakadawa
Babangida Kakadawa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Babangida Kakadawa
Babangida Kakadawa
Songwriter

Lyrics

Yau nayi tagumi
Na rame ban iya cin komai
Allah koro
Allah koro da masoyiyata
Rashin ganin ta na rame
Bana iya cin komai
Yau ga dan talakawa
Yana son ' yar mai kudi
In na biya sadaki
Ni bazana yi lehe ba
Dana biya sadaki
Ni bazana yi lehe ba
Idan taje gidana
Bazan barta a tsuma ba
Dada amma watakil lale
Babanta baya so ba
Mamarta bata so ba
Matan garin ga sunyi yawa
Kuma sun cika tunbul-bul
Kuma basu son aure
Sai sun bidi mai kudi
Idan baka da kudi
Bana baza kayi mata ba
Idan kana da kudi
In sun ganka da mota
Har hotuna suke kaima
Garje bidi mai kwari
Tsoho da kudi yaro
Yaro inba kudi
Yau ya koma tsoho
Ana wata magana jamma'a
Ga wata magana tazo
Wani mai jaki ya in'giji mai goyo
Babbar magana a nan
Ji ana wata magana jamma'a
Ga wata magana tazo
Wani mai jaki ya in'giji mai goyo
Babbar magana a nan
Ji samari
Mai kida kanin Sani
Na dan Maraya
Wakar wa akeyi sai mu
Toh kun gani yana tsinkewa
Banda irin nauwa
Du nogaren daya murde
Ya zama karfen jirgi
Kirar sa sai makerin asali
Siri ka horo nai nai
Gamu
Don da dan haye da dan gado
Bazasu zame dai ba
Yaro bai san yaro ne ba
Yaro bai san yaro ne ba
Sai rasa baba nai
Ko ya rasa mama tai
Zai san yaro ne shi
Kuji dai yana ganin duniyar nan
Tai masa talala harda fadin
Wai sune zasuyi bamu ba
In banda rashin kunya
Mai bidar nama
Me kaishi zuwa gulbi
Kuma hada wukake nai
Me bidan kifi
Me yakaishi zuwa kwata
Me yakaishi zuwa zango
Kuma harda zugun taru
Tsohuwar kura
Mai bidar kashin bango
Wachan mai kan gina
Inta ga mai tsoka
Bazata raga mai ba
Tsohuwar kura
Sai dai kici kanki
Ni baki cina ba yalon
Alhaji Babangida Kakadawa
Mai kidan kanin Sani
Na dan Maraya
Wakar wa akeyi sai mu
Yau nayi tagumi
Na rame ban iya cin komai
A'a ga dan talakawa
Yana son 'yar mai kudi
Dana biya sadaki
Ni bazana yi lehe ba
Idan taje gidana
Bazan barta a tsuma ba
Written by: Babangida Kakadawa
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...