album cover
Shiriya
644
World
Shiriya was released on April 24, 2018 by Apple Media Africa as a part of the album Iconic Sounds of Africa, Vol. 102
album cover
Release DateApril 24, 2018
LabelApple Media Africa
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM95

Credits

Lyrics

Shiriya tazo min inata hawaye da idona
Ni yau shiriya ce tazoman ina kuka
Dakaina na kashe miji na matar da na aura
Umm anci amana ta zuciya bazan yafe ba
Bani afuwa ga wanda ya kashen miji na
Ita dai shiriya ako ina ana Santa
Wanda yake 'kinta sai muce Allah ya kyauta
Nida kaina na yaudari zuciya ta
Nabi santa dai duk abinda take bukata
Gashi yau nayi nadamar bibiyarta
Dariya nayi abaya yau ina kuka
Ita dai shiriya ako ina ana Santa
Wanda yake 'kinta sai muce Allah ya kyauta
Ashe kai kajawo maraicin zuciya ta
Domin rashinsa mijina na azabta
Ya nunan so mun zauna ba mugunta
Ashe dai mutuwarsa tazo dai a silar ka
Ita dai shiriya ako ina ana Santa
Wanda yake 'kinta sai muce Allah ya kyauta
Uh uhmm na iya sani kuka
Hukunci amman dai dai da abinda na shuka
Zuciya na gyara kasa na duka
Nasan cewa dokon wuya shi na 'dauka
Ita dai shiriya ako ina ana Santa
Wanda yake 'kinta sai muce Allah ya kyauta
Ita dai shiriya ako ina ana Santa
Wanda yake 'kinta sai muce Allah ya kyauta
Wanda ya kashen mijina shi nake nema
Fansa na 'dauketa acikin salama
Ya 'dan 'dana inda dadi zayaji shima
Idanuna sunyi rufewa bana shakka
Ita dai shiriya ako ina ana Santa
Wanda yake 'kinta sai muce Allah ya kyauta
Wanda ya kashe shima hukuncinsa kisa
Na yarda komai nawu ayau zana rasa
Haka shine dai-dai shari'a haka ta 'kunsa
Kalla matar da na aura banida fuska
Ita dai shiriya ako ina ana Santa
Wanda yake 'kinta sai muce Allah ya kyauta
Umm matsalar dana shiga ashe kaine kajawo
Kasanya zuciya ta tanayin kai kawo
Ina ka tafi inama dai ka dawo
Dama dai kazo naganka ni na kasheka
Ita dai shiriya ako ina ana Santa
Wanda yake 'kinta sai muce Allah ya kyauta
Ni yau shiriya ce tazoman ina kuka
Dakaina na kashe miji na matar da na aura
Umm anci amana ta zuciya bazan yafe ba
Bani afuwa ga wanda ya kashen miji na
Ita dai shiriya ako ina ana Santa
Wanda yake 'kinta sai muce Allah ya kyauta
Written by: Nura Musa Inuwa
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...