album cover
Dakin So
album cover
Dakin So was released on May 1, 2018 by Apple Media Africa as a part of the album Iconic Sounds of Africa, Vol. 113
May 1, 2018
LabelApple Media Africa
BPM160
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy

Lyrics

Eh burin raina mu zama mata da miji
Dakin 'kauna in na saka ki karki fito
Eh burin raina mu zama mata da miji
Dakin 'kauna in kasakani zanyi zama
'Dakin so buri na masoya su shige
Kogin 'kauna kyau na masoya kar su fito
Eh ka fada mani na fada maka so abinda ya 'kunsa
Sirrikan zuciya dukan raina nabarmaka fansa
Inda rai da rabo cikin so ina muka dosa
So nike ni kaban yadmrda jikin ka na kwanto
Kullun zuciya tana radadi, so ciwo ya zame mani
'Kaunarki cikin jiki da jini, dan Allah ki tausaya mani
Kalaman so biya mani, in na manta tina mani
Ido kuka ya raina
Dakin so buri na masoya su shige
Kogin 'kauna kyau na masoya kar su fito
Eh ka rike ninna rike ka soyayya
Al-'kawarin da mukayo ban karya
In kau ka gujeni kaga sai jinya
A gidanka zaka bani tarbiyya
Inkace nace dakai jin kunya
Inuwa akwai jikin iccen kanya
In ka saman so na sama ban cire kokanto
Dakin so buri na masoya su shige
Kogin 'kauna kyau na masoya kar su fito
Shi so indai yakama mutum, akwai matsala daya fice
Kamar hanta da jini haka za dashi da ruwa kikar yace
Idan na rasaki zan mace tinani nawa zai 'bace
Ki kurbi ruwa na 'kauna
Na taho gunka ina neman kaman alfarma
Banijin komai inba zancenka nazama kurma
Zanji dadi inda kanka kasani hannin dama
Duk abinda kace zanai makashi ko zani azabtu
Umm kin da baibayeni kin sakan sarka
Magana nake ina nake ina yawan saka
Ga amana tawu tashi kiyi damka
So dafinsa ya wuce dafin fika
Warware ni ga wuya na nawu na mika
Masu kushe su dukan su sun mika
Nayi narkewa akan 'kaunarki safe da rana
Dakin so buri na masoya su shige
Kogin 'kauna kyau na masoya kar su fito
Burin raina mu zama mata da miji
Dakin 'kauna in kasakani zanyi zama
'Dakin so buri na masoya su shige
Kogin 'kauna kyau na masoya kar su fito
Written by: Nura Musa Inuwa
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...