Music Video
Credits
PERFORMING ARTISTS
Nura M. Inuwa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
RR
Songwriter
Lyrics
Eh nayi gamo da masoyin gaskiya
'Dan 'kwarai yasani a zuciya
Yashiga raina bazana cireshi ba
Eh yau nasamu ganimar 'diyar kwarai
Tinda kin sakani a zuciya
Kin shiga raina bazana cireki ba
Al'amarin so nesa da marmari
Zuciya zabin ta da ta gano
Sai ta zira koda ba'a fargaba
Eh nayi dashe na shuka an ruwa tsuro na mai kyawu ya fito
Ga limshi a gari iska tana kadawa ina yin anbato
'Karshe gudun zuciya baya tsayawa nazarce na ganni a Sokoto
Bayanan so kiyi sai su sanyaya raina ya daina 'karaurawa
Al'amarin so nesa da marmari
Zuciya zabin ta da ta gano
Sai ta zira koda ba'a fargaba
Mai sanka shi zaisaka a zuciya akan so yadinga 'dawainiya
Harma idan akasi tsakiya yazo baya fushi saidai yai dariya
Kyan yaba kyauta tukuici ne in ba abinyi abita da godiya
Furanni na 'kauna sun fito a lambu kaine mai ban ruwa
Al'amarin so nesa da marmari
Zuciya zabin ta da ta gano
Sai ta zira koda ba'a fargaba
Oh ki rike al-'kawarinki in kika raba 'kauna so zaiyi armashi
Da kinga na daga murya sai ki saita harshenki dole nabar fushi
Duk wanda yaci amanar so wajen hukunci ai masa da garwashi
Yin haka zaya rarrage matsalar masoya su daina jigatuwa
Al'amarin so nesa da marmari
Zuciya zabin ta da ta gano
Sai ta zira koda ba'a fargaba
Al'amarin so nesa da marmari
Zuciya zabin ta da ta gano
Sai ta zira koda ba'a fargaba
Ina abin dace a gurin gudun gidan gara in an sauka gidan zago
Sai jarumi yayiwa so kuka na gaske ya fidda sahun rago
Al'ajabi na wuya nayi kiranka to sai naga ka bugo
Na kada kai nace waishin taya akai hakan keyin faruwa
Al'amarin so nesa da marmari
Zuciya zabin ta da ta gano
Sai ta zira koda ba'a fargaba
Eh miye abin mamaki tinda dai zukatanmu sun mana hanzari
Ko a ina kike to da zaki waiwaya zakiga to ina wannan wuri
Da zuciya ta da takinsuna a tare so ya saka masu sasari
Ko magana inzakiyi naiysi fitowa layi 'daya mai hawa
Al'amarin so nesa da marmari
Zuciya zabin ta da ta gano
Sai ta zira koda ba'a fargaba
Alfarma 'daya zakai in naimaka laifi karkai mani hargitsi
Zamuyi zaben hidda gwanana mije dan zuba mata 'yan hatsi
Rana bazan manta dakai ba duka wuya kokuma tsannani
Dani dakai wakilai ne gun masoya sunan mu na rayuwa
Al'amarin so nesa da marmari
Zuciya zabin ta da ta gano
Sai ta zira koda ba'a fargaba
Eh nayi gamo da masoyin gaskiya
'Dan 'kwarai yasani a zuciya
Yashiga raina bazana cireshi ba
Eh yau nasamu ganimar 'diyar kwarai
Tinda kin sakani a zuciya
Kin shiga raina bazana cireki ba
Al'amarin so nesa da marmari
Zuciya zabin ta da ta gano
Sai ta zira koda ba'a fargaba
Writer(s): Rr
Lyrics powered by www.musixmatch.com