制作

出演艺人
Umar M Sharif
Umar M Sharif
表演者
作曲和作词
Umar M Sharif
Umar M Sharif
作曲

歌词

Sinadari na so makamashi
Rura zuciyata suke yi
A sannu sun zamo garwashi
Kiyo agaji
Sinadari na so makamashi
Rura zuciyata suke yi
A sannu sun zamo garwashi
Kayo agaji
Soyayya a zuci nake ruri kece zaki ban (makamashi)
Hayaki wutar taki tashi ki tallafa kimin (makamashi)
Kece kadai sinadari
Zuciya take buri
Karaso kizo da hanzari
Kar in sha wuya
Kishi in kina ji taho ga ruwa
Babu mai taba ki tunda nine garkuwa
Kaunar ki a duk jikina yayi yaduwa
Babu kuskure in na kira ki kainuwa
A duniyar masoya kin zam
Sarauniyar cikin fadar
Kici abinci kiyo dam-dam
Muje mu rausaya
Wannan halitta mecece?
Ba'a gani da ido shin wacece?
Hannu bai kama ta koko iska ce?
Sai dai ka jita a jikin ka tayi kwance
A suna an kira ta soyayya ce
Ta shige jikina tayo kwance
Ni kadai nasan ciwo na
Damuwar cikin rai na
Maganin ta sai watarana
Wai yaushe zata zo?
In babu ke a duniyar nan
Sai dai in sha ruwan guban nan
Zan more idan kina nan
Farin ciki ya samu kenan
Har abada bazan manta ki ba
Kina cikin raina baki kaura ba
Kece komai nawa
Farin ciki na gani ga shi
Sanyin ido nake kiran shi
Ko zuciya tana yaba shi
Kwayun halin sa bai da kyashi
Sinadari na so makamashi (sinadari na so makamashi)
Rura zuciyata suke yi (rura zuciyata suke yi)
A sannu sun zamo garwashi (a sannu sun zamo garwashi)
Kiyo agaji (kayo agaji)
Written by: Umar M Sharif
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...