歌词
Hhmm to sirrin zuciya
Ya fito fila haka inda na tambaya aka ban amsa
Ke ce zinariya
Ma'ana mai haske tunda idanu da zuciya sun ƙosa
Ni kai ne zaɓina
Kuma haskina mai kore duhu daga sashina
Sirrin zuciya
Ni ina so in ji ɗumin ƙauna
Tunda na gama so a gare ka na furta muradina
Sirrin zuciya
Ina sonka, ina sonka, nima zan so ka ji tausayina
Sirrin zuciya
Kai ne taurarona
Ma'ana mai haske ka idanu da zuciya sun ƙosa
Hhmmm! Na ba ki dukkan yarda
Ki aminta dashen da mukai ya tsiro kuma yayi huda
Sirrin zuciya
Dan Allah ki jaddada, mu rayu at are da ke abada
Sirrin zuciya
Ke ma in kin yarda sanarwa iyaye su yi shaida
Sirrin zuciya
Kar ki ki mini kuskunda, komai kika ce ba kya so na fasa
To sirrin zuciya
Ya fito fila haka inda na tambaya aka ban amsa
Kai ne tauraro na
Ma'ana mai haske tunda idanu da zuciya sun ƙosa
Uhm! to sirrin zuciya
To sirrin zuciya
Haka inda na tambaya aka ban
Dukkanin amsata
Ke ce zinariya
Kai ne jagora
Kin ga idanu da zuciya sun ƙosa
Ha-hah-hah-a'a
Eh-he-yeh-hey-yeh-heh
Nagode hubbi na
Mai kore ƙishi da ruwan ƙauna
Kin sarke tunani na
Ke ce ƙarshen labarina
Amjad records
Midget mix
Written by: hamisu said yusuf


