歌词
Garai ni kin zamo min cikon buri
A rayuwata in na ganki na huta
Garai ni ka zamo min cikon buri
A rayuwata in na ganka na huta
Kowa mafarinsa ne soyayya
A duniya nima na shaida
Dadin ta ne ya sa na riqe hujja
Na so garai ni ga kyautargwanda
Kowa da tashi ni ke na kama
A zuciya ta komai na kauda
Ance in barki ni na ce a a
Domin dani dake munyi agenda
A rayuwata komai na samu
Kullum batun ki shi nayo bita
Yawan ganin ka baisa in gajiya
Koka garai ni kunne na hurai
Raina garai ka fansa ga ajiya
Tunda komai ka tarai
Nidai hasasshe kunne nike miya
Ba ayin hadi da bature
Masoya sun ka che mana sannuku
Mun daina soyayya kun kurai
Mu gazgata su mu ma mun amsa
Dani da kai nasan da fahimta
Kowa da nashi yake takama
Nidai da ke nake yi
Kyawu a kanki an gama
Sa ni a rai in fake
Yaki taho nan da takama
Har inda ni nake
Zan dauki duk wani hiddima
Naki ki wartsake
Wannan hakane nasaba
Wajibi inyi bajinta
Babu sauri jirkinta
Kai nake wa janjani
Kaga layi ya shata
A kanka ba mai rai na ni
Na riqe so ba mai kwata
Ni taka ce nai imani
Zan ma abunda duk ya kamata
Domin gujewa mai muni
Naga nasara mu take harara
Wallahi nima na gan ta
Written by: Abdul D One


