制作

歌词

Tafiya ta, nakusa kai wa
Kwanakina, suna wucewa
Cikin jakata, ban sani ba
Guzirina, tayaya zan iske gida
Buri na raina shine in sai gidaje
Daki na kwana,in sa gadaje
Motar hawana, duk inda zanje
Ana rakona, comboy kamar kudaje
Inata fankama, inata cije-cije
In canza kaya, kullum in gyara saje
Bana tunawa, da inda nai fitowa
Namanta cewa, watarana zan komawa
Na cinye komai, bani tattalawa
Koda sakoma, bani turawa
Na yanki visa, ta kusa karkarewa
Kuma babu dama, bare inyo dadawa
Wayyo ni, wayyo
Wayyo ni, wayyo
Wayyo ni, wayyo
Ya zanayo dakaina
Akwai gida nabiyu inda zani kwanta
Gidan da ba'a zama ciki da mata
Babu iyaya 'ya'ya bare makwabta
Abinda nazo, dashi zani zanta
Abinda ni na rubuta shi zan karanta
Bawanda zaya aje bare na sata
In nayi kirki, ba mai yi man mugunta
Wayyo ni, wayyo
Wayyo ni, wayyo
Wayyo ni, wayyo
Ya zanayo dakaina
Allah yaso ni, tunda na ankare
Sai in kara kaimin nema, cikin darare
In ci lokacina, kafin ya karkare
Abinda nasamu, sai in tattali
In aika gida, in naje mu warware
Gida na ukku, in da ba'a boye-boye
Duk wanda ya mutu, rannan ka ganshi raye
Kowa a girme, ba wanda ke a goye
Wasu suyita murna, wasu suyi zubar hawaye
Abinda ka aika, shi zaka sama
Mu aika alkhairi, muje mu sama
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...