歌词
Rub master
AD music studio
Me zanyi in fanshi kai na?
A gareki in fanshi rai na
Bacci yana gagara na
Kinyi carap kin saida raina
Ina ta kokari in gyara
Ina ta kokari in tsara
Abinda zai saki murna har farincikinki ya zauna
Tarairaya
Tarairaya
Tarairaya nake so tarairaya
Ba abinda ba zan baki ba
Babu inda bazan kaiki ba
Ba abinda ba zanyi a kanki ba masoyiya onana
Ba abinda ba zan baka ba
Babu inda bazan kaika ba
Ba abinda ba zanyi a kanka ba masoyina onana
Idan na fada maki kya yarda
Son ki a raina akwai tsada
Ta wace hanya zan shaida?
Ungo jaridarki karanta
Kin san
Ke naiwa tanajin kaina
Dangi, da 'yan uwa gareni sun zama shaida ne
Ance ra'ayin riga
Kyallenki na hanga
Tushen kida ganga
Goma karshen kirga
Akwai wasu labaru
Wutar son ki ta ruru
Abuja zuwa Karu
Mata sun jeru
Amma basu kaiki ba
Ban ga mace kamar ki ba
Ba zani canza tsari ba
Da son ki zan rayu
Ba abinda ba zan baka ba
Babu inda bazan kaika ba
Ba abinda ba zanyi a kanka ba masoyina onana
Ba abinda ba zan baki ba
Babu inda bazan kaiki ba
Ba abinda ba zanyi a kanki ba masoyiya onana
Written by: abdulkadir tajuddeen