歌词
[Intro]
(AMG Boy Records)
Alo, alo
Alo, alo
Ayyah, kece ɗaya (Eh mana)
[Verse 1]
Kina nan, kina nan
Kina nan a zuciyata
Kina nan, kina nan
Kina nan a duniya ta
[Verse 2]
In zanyi aure, kece tilo gida na
Kece kuɗi na
Kece abin marmari na
Kece ruwa na
Kece dai armashi na
Ban da komai, ban da kowa, ke kike kore ƙishi na
[Chorus]
Kyakkyawa
Kece kyakkyawa (Ke nake so)
Kyakkyawa
Yarinya kyakkyawa (Ke nake so)
Kyakkyawa
Kece kyakkyawa (Ke nake so)
Kyakkyawa
Yarinya kyakkyawa (Ke nake so)
[Verse 3]
In dai a kan ki ne komai ki san zanyi shi
In dai zan faranta ran ki, zan ci koda bashi
Aikin ƙarfi nayi, ko zan tsaya numfashi
Ko duka zana ci, gare ki zan kai toshi
[Verse 4]
A ƙauna na tsunduma
Nake jure tsangwama
Ina son ki an gama
Zan ci koda kwaɗon rama
Fito nayi sallama
Wa juna mu runguma
[Verse 5]
Indai kin tashi lafiya
Toh ina jin farin ciki
Na so ki, kema kin so ni
Na ba ki, kema kin bani
Ni banda abinda zan baki ʼyanmata
Ammah zan baki farin ciki, cikin ƙwallata
Cikin ƙwallata
[Chorus]
Kyakkyawa
Kece kyakkyawa (Ke nake so)
Kyakkyawa
Yarinya kyakkyawa (Ke nake so)
Kyakkyawa
Kece kyakkyawa (Ke nake so)
Kyakkyawa
Yarinya kyakkyawa (Ke nake so)
[Verse 6]
Ke kika faɗa da bakin ki
Kika nuna da hannun ki
Nayi murnar zuwan naki
Je ki na tsaya a bayan ki
Watarana sai labari
Sai labari
Watarana sai labari
Labari
Ke nake so kyakkyawa
Written by: Auta mg boy


