Lyrics

So ya zamo kadarar zuci Ni kawai ki mutunta ni Ga guri miko guna zuci dan kece asalin farko Nima burin raina da kai a ce, "Za ai min baiko" In kin kai na fara kinga koh na hau sai na sauko Nima din hakane ja ni kai ne hannaye na na miko Wanda yake so na zana baiwa kauna ba makiyi na ba Indai gaka kusa na masoyi baza a ga fushi na ba Kukan zuciya shi ne a ce bazan sauke ki gida na ba Na dau alkawari ban barin ka alkhairin ka in na girma Mun ratsa dare naga yara har sun nemi gadon bacci Lissafin ka da ni daya ne kaban komai ka ci sai naci Tunkaho da dagawa har daukaka har ya zama ganganci Kai dai dubi ado na masoyi my baby nai turanci Dake nake in ba ke toh a bar kira na ma Farin masoyi lallai inuwar ka na fake nima A duniya tsari na kalar ki shi nake nema Naga shimfidar fuska ai ta wuce ta tabarma Kin zamo madubin zuciya ke kadai nake kallo Farin wata in har kaga zara dole zai bullo Kar ki bari a ta dalilin son ki ayi min gwalo Na kulle ruhi karba ga dan makuli zan cillo Wayyo ni duniya dadi Masoyiya zo saurari lafazi na Kina da kyau babu kamar ki a guri na Ki rike so bana so a ganmu ra-ra In banda ke toh wa zan wa tambari na? Na dauki alkawar' nima ban saka ka kuka Rabo da kai sai dai in wuce ma yanka A zuciya tabbas babu madadin ka A ko ina ban tsoron na bayyana ka Ni taka ce gaba daya Komai kika ce ne ni baza naki ba Ka bani zumar so kar ka bani guba Da nai ki naki yana dada sani haw jazaba A kanka fah sai da matuwa ta raba Dole sai da amana so yake tafiya Ko mai ka saka ni a ki ka zana iya Wuya ko dadi tare za mu tsaya Ina ra'ayin ka a zuciya kaji ba karya Ka mutunta ni (Mixed kobincus) Kar ka saka ni a rudani
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out