Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Fresh Emir
Fresh Emir
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Adam Abdullahi Emir
Adam Abdullahi Emir
Songwriter

Lyrics

Aku mai bakin magana
A yau ma nazo zanyi magana
A yau magana, a yau da magana
A yau da magana
Kaine fresh emir aku sarkin zance?
Ance komai wuyar kullin gaskiya ka kan kwance
Toh nazo yin bayani babu kauce-kauce
In na tambaya ka yanzu, shin miye zakace?
Wane kallo gwamanati ke ma 'yan arewa?
Wawaye, banzaye, ajawuka
Sakarkaru, dabbobin kwantarwa a yanka
Wa'inda basu san kansu ba dau hakika
Kallon da suke mana kenan amma yanzu mun farka
Yanzu ta fito fili ba san mu ake ba
Ta tabatta mun gane ba tamu suke ba
Tunda ba amfani suke mana ba
Toh su sani lokaci yayi da baza mu raga ba
Kuna gani sai kashe mu akeyi
Amma kunji ko maganan sunayi?
Sun maida mu kamar shanu da makiyayi
Da saninsu wallahi ake maishemu marayi
Boko haram a arewa akeyi
Kidnapping a arewa akeyi
Kauyikanmu bude wuta akeyi
In zamu fita fidda ran dawowa gida mukeyi
Na lura raina mana hankali akeyi
Tayaya za'a samu bindiga gurin makiyayi?
Kuma bama bindiga ta da ba ta yayi
Toh mun gaji da wannan rainin wayau
In za'a kashenu a fito fili ayi babu boyo
Ba tsoronta muke ba muna ma oyoyo
Bamu fara furta gaskiyar ba sai da muka shiryo
Ni Adam Abdullah emir dan arewa
Na rantse da Allah babu wanda zan kara ragawa
Madafan iko 87 arewa amma haryanu ace ran mu ma kun kasa tsarewa
Asibitocin ba magani
Ba titi mata masu nakuda sun bani
Babu wutan lantarki da more zamani
Yunwa ta addabi al-umma kuna gani
Mu a gurinmu sunayen ku marassa amfani
Bana dai na fada dama kara mukeyi
Yanzu babu maganar karan batun kishi mukeyi
Ina kira ga mawakan arewa
Da yan film din arewa
Marubutan arewa
Masu barkwanci da suke cikin arewa
Bama lissafi ba duk mai daukakan cikin arewa
Da wanda suke da hanyar tura sako arewa
Mu fito kwanmu da kwalkwata nuna kishin arewa
Dan naga mun fara zama maroka
Kwadayi yasa mun tsinci gaskiya mun kasa dauka
Mu kawar da ido kan kiye za'a baka
Dan ko sisin su ka daina ci in an daina yayinka
Saboda haka mai bacci ya farka
Fito na fito ka fito mu ceci yan uwanka
Aku mai bakin magana
A yau nazo na gama magana
Written by: Adam Abdullahi Emir
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...