Lyrics
BASH NEH PHA
BASH NEH PHA
BASH NEH PHA
Zuma record
BASH NEH PHA
Menene mai sa farinciku a koda yaushe?
Menene mai jawo talaka cin miyan taushe?
Menene mai sa farko kuma takoma karshe?
Menene mai muke bukata ne a koda yaushe?
Menene mai saka shugaban kasa a bushe?
Menene mai saka dan Adam zama a koshe?
Kar kuce man ni ina ta zuba ku kuna toshe
Menene mai cinye tattali taci adashe?
Menene mai sa acinte tattali a ci a kwace
Inata tambaya, please my people answer that
Abun babba my people ma they using that
Kubani fili dan mama let me scatter that
Miye sai dashi ake ilimi? (Lafiya ce)
Miye sai dashi ake addini? (Lafiya ce)
Miye sai dashi ake soyayya? (Lafiya ce)
Miye sai dashi ake mulki? (Lafiya ce)
Miye sai dashi a haifi yara? (Lafiya ce)
Miye sai dashi ake zalinci? (Lafiya ce)
Miye sai dashi ake ilimi? (Lafiya ce)
Miye yafi kudi dadi? (Lafiya ce)
Miye yafi aure dadi? (Lafiya ce)
Miye yafi daukaka dadi? (Bash neh pha)
Lafiya na gaba da komai true babu shakka
In babu ita dadi komai dukiyanka
Idan da ita babu kwandala kayi sha'aninka
Mai hankali ka roki lafiya kan arzikinka
Ko daukaka ma sai da lafiya ne za'a sanka
Mai kaunar tuki inda lafiya zai tuka tanka
Noma ne takamanku sai da lafiya a shuka
Lafiya ce mai core hankali ta sanya hauka
A neman lafiya kaga mutum ya shafa toka
Akwai abinda yafi lafiya ne je ka dauka
Kana da kudi da mulki gwanin taka doka
Allah ya rabaka da lafiya me zaka taka
Kana ilimi da yawa a cike a kanka
Kayi tunani in babu lafiya menene ranka
Kana yin soyayya da yarinya mai mugun son ka
Kuma kana da baiwa ko ina kowa na son ka
Kuma kanada magoya baya duk suna bin ka
Abin da yafi duka dadi shine lafiyanka
In ka samu lafiya dan mama kayi sha'aninka
Idan kaga kana yawan surutu (lafiya ce)
Idan kaga mai yawan dariya (lafiya ce)
Bazan fada ba yin gulma (lafiya ce)
Halinka yin tsokana (lafiya ce)
Gafe muje biki (lafiya ce)
Bakada aiki sai chatting (lafiya ce)
Kai kwararre ne a ado (lafiya ce)
Miye dalilin jin waka (lafiya ce)
Toh nima mai yin wakan (lafiya ce)
Bash ne
Sai da lafiya ne muke dandali
Kaga ba wiya mun fita gantali
Don lafiya ne mata suke kyallyali
Har a gidan biki ma suke dandali
Suyita yin rawa like ba hankali
Lafiya na sa aci ba cokali
Lafiya gatan bawa jahili
Komai a kulle lafiya makulli lafiya
Aikin baiwa da hankali
Dan mama kuji waka a hankali
(Dan mama kuji waka a hankali)
Miye sai dashi ake ilimi? (Eh)
Miye sai dashi ake addini? (Lafiya ce)
Miye sai dashi ake soyayya? (Lafiya ce)
Miye sai dashi ake mulki? (Lafiya ce)
Miye sai dashi a haifi yara? (Lafiya ce)
Miye sai dashi ake zalinci? (Lafiya ce)
Miye sai dashi ake ilimi? (Lafiya ce)
Miye yafi kudi dadi? (Lafiya ce)
Miye yafi aure dadi? (Lafiya ce)
Miye yafi daukaka dadi? (Bash neh pha)
Written by: Bashir Halliru


