Lyrics

Laraba-Laraba, Laraba sarauniyar mata Laraba-Laraba 'yar sarkin masar zani nema Laraba-Laraba, Laraba sarauniyar mata Laraba-Laraba 'yar sarkin masar zaka nema Eh zani garin Masar 'yan uwa Inga sarauniya Laraba Ga kura da zaki cikin tawaga Kerkece nan har dabona Amma haka zani (a'a kar kaje) Sai na shiga (dawo karkaje) Na sha ganin Laraba a mafarkina in nayi barci Soyayya ce tsakanina da sarauniya Laraba Kuma munyi al-'kawarin aure a mafarkin nai tunowa To yaya zanayi Bari Tasi'u hakuri zakayi A'a tafiyar shekara talatin bata hanani naje ganin 'yar sarki Laraba-Laraba, Laraba sarauniyar mata Laraba-Laraba 'yar sarkin masar zaka nema Ta nadi zuciya Laraba Yarda na ganki ya sahiba Nayi shiri naje cen gari na masar Aurenki yau zani nema Bari sai na tafi (a'a karkaje) Ko zansha wuya (dawo karkaje) Tafiya nake babu cin yau da na gobe ga 'kishirwa Dajin akwai hatsari na mutanen 'boye masu kauda kowa Daga nesa na hangi wasu zaune a kan dawakai tahowa To ya ya zanayi Bari Tasi'u hakuri zakayi A'a tsanani wuya azaba baya hanani naje ganin 'yar sarki Laraba-Laraba, Laraba sarauniyar mata Laraba-Laraba 'yar sarkin masar zaka nema Laraba-Laraba, Laraba sarauniyar mata Laraba-Laraba 'yar sarkin masar zaka nema Naga mutanen na tahowa Nazaci taimako zasu zoyi Wai ashe kame sukeyi Na 'dan Adam su sayar da bayi Nai 'kokari in kwaci kaina na rasa 'yan uwa ya zanyi Haka dai zan tafi A'a karkaje Sai na shiga Dawo kar kaje An saidani ne garin wani sarki wanda baisan mutane Da wuta mukeyi kamar dabbobi shikwa yay him a zaune Kullun tunani ne raina wai yazanyi in 'kwace kaina To yaya zanayi Bari Tasi'u hakuri zakayi A'a wahala ta garinga ta isa, nidai sai naje ganin 'yar sarki Laraba-Laraba, Laraba sarauniyar mata Laraba-Laraba 'yar sarkin masar zaka nema Laraba-Laraba, Laraba sarauniyar mata Laraba-Laraba 'yar sarkin masar zana nema Laraba-Laraba, Laraba sarauniyar mata Laraba-Laraba 'yar sarkin masar zaka nema
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out