Music Video
Music Video
Credits
PERFORMING ARTISTS
Umar M Sharif
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Umar M Sharif
Composer
Lyrics
[Verse 1]
La la la (Garinmu da nisa)
La la la (Garinmu da nisa, garinmu da nisa)
Garinmu da nisa
[Verse 2]
Uhm! Soyayya na yi niyya da ke za ni daura
Fuskata ta nuna ke nake so kowa ya yi lura
Komai nau in ba da a ba ni ke haka ban da asara
Na zam wata ke ko Zahra Zahra
Samari sai ku yi hattara ni take jira
[Verse 3]
Zuciyata babu kowa tilo kai ne a ciki nai rufewa
Na sa tsaro gareta
Babu mai rabata
Kai ne ki Sarauta, ka zamo jagaba
[Verse 4]
Garinmu da nisa tazara sam ba za ta hana ni na zo ba
Idanu ganinki suke marari ba zan so rabuwa da ke ba
Garinmu da nisa tazara sam ba za ta hana ni na zo ba
Idanu ganinka suke marari ba zan so rabuwa da ke ba
[Verse 5]
E! Wanda ya yi so domin Allah shi ya more a rayuwa
Wanda yai azumin ya yi sallah lahira ba ya kishin ruwa
Lammura in ka bar su ga Allah zai biya ma duk daren dadewa
[Verse 6]
Shi yai hadimi na soyayya
Ga shi aure muna niyya
In kira ki sarauniya
[Verse 7]
Kai ko Sarki a soyayya
Ka zamo tauraro cikin maza
Don fitowarka ke sa su girgiza
Na aminta da kai aure da kai
Nake sa raina
[Verse 8]
Garinmu da nisa tazara sam ba za ta hana ni na zo ba
Idanu ganinki suke marari ba zan so rabuwa da ke ba
Garinmu da nisa tazara sam ba za ta hana ni na zo ba
Idanu ganinka suke marari ba zan so rabuwa da ke ba
[Verse 9]
Garin masoyi ba ya nisa
Da sannu sannu yau ga ni a cikinsa
Tunda ka zo ga ni na zo mu gaisa
Na tarbe ka oyoyo mutya na tausa
[Verse 10]
Yanzu ban da sukuni
Kullum sai tunani
Ko da a ma'auni
Misali a sa ni
Zai ba da bayani
Abin da ya kawo ni
[Verse 11]
Sonki ne a raina, dare da rana
Hope nake mu zauna buri a raina
Ni da kai na zauna buri a raina
[Verse 12]
Eh! Garinmu da nisa tazara sam ba za ta hana ni na zo ba
Idanu ganinki suke marari ba zan so rabuwa da ke ba
Garinmu da nisa tazara sam ba za ta hana ni na zo ba
Idanu ganinka suke marari ba zan so rabuwa da ke ba
Written by: Umar M Sharif