Music Video

Featured In

Credits

PERFORMING ARTISTS
Umar M Sharif
Umar M Sharif
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Umar M Sharif
Umar M Sharif
Composer

Lyrics

Madubi, madubin duba na (wayyo, oh) Madubi, madubin duba na (lalalala) Madubi, madubin duba na Mahakurci mai dace ne inda yawancin kwana Zabin Allah daya ne dai madubin duba nae Mahakurci mai dace ne inda yawancin kwana Abinda nake so na samu madubin dubana Mahakurci mai dace ne inda yawancin kwana Zabin Allah shine zabi ba zabin mutum ba Na bude idanu da gani menene kallo na Mafarki ne ko gaske jama'a kuyi duba na Wanda nake so ya fuskance ni na cika buri na Tafiya ta kama ni masoyi na hada kaya na Mafarki na ya zama gaske ina jindadi na Kunya ta kamani masoyi zo kayi kallo na Mahakurci mai dace ne inda yawancin kwana Zabin Allah shine zabi ba zabin mutum ba Dukkan mahakurci shine mawadaci yanmata Koda bawa ne watarana zai zamto dan gata Hakurin da mukayi yau mun samu zabi mai nagarta Zabin Allah shine zabi yau na fahimta Mahakurci shine mawadaci mun zama yan gata Mahakurci mai dace ne inda yawancin kwana Zabin Allah shine zabi ba zabin mutum ba Yau na samu, natsuwa raina yayi kwantawa Bani da damu, fara'a ta ba kakkautawa Kai na samu, na zaba bana canzawa Allah kai mu, randa mutane za suyi shaidawa Jindadin mu, auren mu idan aka daurawa Mahakurci mai dace ne inda yawancin kwana Zabin Allah shine zabi ba zabin mutum ba Kin rinjaye, a guri na kin zama yar gata Ba tawaye, na yarda ki zamto mata ta Babu hawaye, a cikin lamarin da fahimta Harda iyaye, nayi mana kyakkyawan fata Sama lulale, na taka rawa dube ni ki ganta Mahakurci mai dace ne inda yawancin kwana Zabin Allah shine zabi ba zabin mutum ba Buri na masoya aure ayi daurawa In na fara biyayya sam-sam ba dainawa In kinyi hakan, toh lallai kin burgewa Mai zaya hana, alkawari nayi daukewa Ke kika furta, ya zama lallai kiyi cikawa Ban sabawa, nasan nayi babban dace
Writer(s): Umar M Sharif Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out