album cover
Daga Yarda
9,989
Vocal
Daga Yarda was released on February 23, 2020 by Amjad Records as a part of the album Daga Yarda - Single
album cover
Release DateFebruary 23, 2020
LabelAmjad Records
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM130

Credits

COMPOSITION & LYRICS
hamisu said yusuf
hamisu said yusuf
Songwriter

Lyrics

[Intro]
Zaharaddeen on the beat
[Verse 1]
Daga yarda aminci ke samuwa
Dama za ki ba ni damar yin ambato
[Verse 2]
Daga yarda aminci ke samuwa
Dama za ka ba ni damar yin ambato
[Verse 3]
In dai zantukanki ne zanyi da sauri sauri
Kuma in tsabtace su karɓesu a tsari tsari
Inbigi zuciyar da raʼayinta da kwari kwari
Ke ma kin sani ina sonki da gaskiya
Dama za ki ba ni don in daɗa juriya
[Verse 4]
Ni na fi sonka duniya za nai ikirari
Burina ka ba ni so kar da ka minni gori
Daga ni har kai ka ga soyayya ce mafari
Shi mahaɗin rabo masoyi ne gaskiya
In dai za mu ɗauki hanya miƙaƙƙiya
[Verse 5]
Kalmominki ne suke ƙara rikirkitani
In ta farin cikin da ba na yi mai maʼauni
Wanda yake biɗar ganin so to ya zo ya ganni
Fatana in sami yardarki gaba ɗaya
Ba a sauya so bare ai masa zamiya
[Verse 6]
Ka fahimce ni don daren jiya na kasa bacci
Da tunaninka zuciyata kuma babu ƙunci
Sai hasashen irin kalamanka da babu ɗaci
Bari ka ji ka mayar da ni autar duniya
Inda na saka kumma ni ka ɗara zuciya
[Verse 7]
Maza ki kula mu toshe baki na magulmata
Masu shirin shiga tsakani namu ba zata
Don na san da ni a rai naki na gaskata
Kai ne fassarar mafarkina gaba ɗaya
Na gode da jin kalaman ki masoyiya
[Outro]
Mid get mix
Daga yarda aminci ke samuwa
Dama za ka ba ni damar yin ambato
Written by: hamisu said yusuf
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...