Lyrics
[Verse 1]
Ah riba ta so ce ƙirga
Ah ba ta da daraja a jajanta
Uhm ga ke a bar yi min burga
Ah ƙarshen ƙure ado riga
Ah in mun faɗa mu sasanta
Ah ƙwarya tana da gurbinta
Ha ha ga ƙaunarki ta yi min rumfa
Da-da-da-dame ni kalli don ƙauna, sai na daddafa
[Verse 2]
Eh, kowa da tasa ni kun ga gwanata
To ba a yi sharhi ba
Kai ma da taka ai ba ta ɗara tau ba
To ba a yi ta ji ba
Kowa gwaninsa ke yi wa maraba
Ah ni ma da tawa don ban yi bara ba
Ah don haka na ce zuru ba ta ci zuru ba, ba za a fara ba
[Verse 3]
Hey ga maganin da ba a haɗa shi da kanwa
Ki ba ni soyayya
Sanya a ranka ba a haɗa ki da kowa
Aradu ko gayya
Kai ne da fari ni ke da idarwa
Ni ke da jarumi mai na sanarwa
Mai ba ni babu shi ke da iyawa
Ki sani kan hanya
Ga malami a bar mai dubawa
Ina ina sa'a
Ha ina ina sa'a
[Bridge]
Hey a so ban yi zaune ba ban baya
Ina zaki jani na iya zarya
Ina za ni ba ka ka ɗara kowa
Idan an taɓa ka zan bi da garwa
[Verse 4]
Ehh, ƙauna ƙauna ƙauna me riba kanta nake kullum
Zauna zauna zauna ga riba sai ka riƙe lalo
To zauna gun annuri na kar ka yi min nisa
Ke ce ruhina linzamina in da nake kwana
Kai zan alkinta na ƙuƙuta ba a rufe suna
Tuwona maina sai ƙauna nai dake dai
Baban burina samu na yi min daidai
Yarda kin yarda sirrina kin karɓa duk
Yarda na yarda sirrinka na karɓa duk
Adana mai sona
Zan adana ma, ha
Written by: Muhammad Khalid Yunus